1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

COP28: Scholz ya gabatar da kokarin Jamus kan muhalli

December 2, 2023

Shugaban na Jamus ya ce duniya za ta iya rage makamashin da ke cutar da yanayi, yana mai bayar da misali da kasarsa wacce ya ce ta kashe Euro biliyan shida wajen samar da makamashi da za a iya sabuntawa.

https://p.dw.com/p/4Zi8h
Hoto: AP/Rafiq Maqbool/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi kira ga kasashen duniya su rubanya kokarin da suke a kokarin samar da makamashin da ake iya sabuntawa daga nan zuwa shekara ta 2030. Scholz ya fadi haka ne a yayin da yake jawabi a babban taron duniya kan sauyin yanayi, COP28 da ke gudana yanzu haka a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Baya ga shugaban gwamnatin Jamus sauran kasashen da suka yi jawabi a baya-bayan nan sun hada da Faransa da Amirka da kowanensu ya bayar da shawarwarin yadda yake ganin za a kara alkinta muhalli tare da shan alwashin yin duk mai yiwuwar wajen ganin an dakatar da tasirin sauyin yanayi da ke ci gaba da yi wa Mutum da Duniyarsa barazana.