1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na yin nazari a kan sauyin yanayi

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
November 30, 2023

Yayin da aka bude taron sauyi yanayi na MDD, COP28. Taron na bana ya mayar da hankali ne kan batun rage dumamar da duniya ke fuskanta da ma yadda za a daina amfani da man fetur.

https://p.dw.com/p/4Zdku
Hoto: Amr Alfiky/REUTERS

  Taron na bana dai ana tunanin an dauki kasar da ba ta dace ba, kasancewar Hadaddiyar Daular Larabawa na zaman guda cikin manyan kasashe da ke fitar da man fetur a duniya. hakan dai ta sanya ana ganin tamkar ba kasar da ta da ce a gudanar da wannan taron ba ke nan. Shugaban taron sauyin yanayin na COP27 Sameh Shoukry ne dai ya damka kambun taron na bana na COP28 ga Shugaba Sultan Ahmed al-Jaber na Hdaddiyar Daular Larabawan, wanda shi kuma yayin jawabinsa na bude taron ya sha alwashin ganin an cimma matsaya a wajen rage dumamar duniya da ma batun amfani da man fetur din da ke fitar da iska mai gurbaata muhalli yana mai cewa:

Duniya na cikin mummunar hadari na ambaliya saboda sauyin yanayi

Pakistan | Gefahr für Bergdörfer durch schmelzende Gletscher
Hoto: Akhtar Soomro/REUTERS

"Mu bari tarihi ya nuna yadda wannan gwamnati ta dauki matakin tattaunawa da kamfanonin mai da iskar gas, abin da ya kasance ba mai sauki ba. Sai dai a yau kamfanonin nan, sun amince da kawo karshen fitar da sinadarin methane da ke gurbata muhalli nan da shekara ta   2030. A yanzu kuma a karon farko, kamfanonin mai na cikin gida, sun amince da kawo karshen fitar da sinadarin nan da shekara ta 2050. Ina mai matukar farin cikin yadda suka amince su shiga cikin wannan tsarin na kawwo sauyi, sai dai zan iya cewa hakan bai isa ba koda yake na yi imanin za su iya yin fiye da hakan sosai."

Fatali da kiraye-kirayen yin watsi da yin amfani da man fetur

Großbritannien Wales | Schornstein
Hoto: blickwinkel/IMAGO

Kididdigar da aka nunar a taron na  COP28 na bana dai ta nunar da cewa sama da ayyukan man fetur da iskar gas 400 ne aka amince da su a duniya cikin shekaru biyun da suka gabata, duk da kiraye-kirayen yin watsi da duk wani abu da ya shafi fitar da gurbatacciyar iska. Yayin da gurbatacciyar iskar da masana'antu ke fitarwa ke ci gaba da yin barazana ga duniya, kasashen da ke halartar taron COP28 na birnin Dubai din na fuskantar matsin lamba kan lallai su tabbatar da ganin an ciima aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris da ta amince da rage dumamar da duniya ke fuskanta zuwa digiri daya da digo biyar. Sai dai kuma matasa masu rajin kare muhalli sun kara jaddada muhimmancin ba su damar yin zanga-zanga a wuraren da irin wadannan taruka ke gudana. Kungiyar "Youth Activists for Climate Actions Philippines" da ke rajin kare muhalli, ta koka kan yadda ta ce mahukuntan Dubai sun takaita musu damar yin zanga-zangar.

Masu fafutikar kare muhali na matsa kaimi wajen samun daidaituwar baki a taron

Deutschland Klimaprotest Last Generation in Berlin
Hoto: Nadja Wohlleben/REUTERS

Kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawan dai, ta musanta zargin wadannan kungiyoyi masu rajin kare muhallin, inda ta ce tana maraba da duk wata tattaunawa mai amfani kana za a bai wa duka mahalarta taron na COP28 damar yin zanga-zangar lumana domin bayyana ra'ayoyinsu. Duk da matashiya  Mitzi Joneele Tan ta kungiyar "Youth Activists for Climate Actions Philippines" da ke rajin kare muhalli ta bayyana yadda aka sanya musu tarnaki mai yawa wajen gudanar da zanga-zangar da ta ce abin damuwa ne, sai dai tana da fata:

Takaita fitar da iskar gas a duniya zai rage gurbata muhali

Ukraine Boyarka | Gaspumpstation
Hoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images

Ta ce: "Yayin COP28 ko kuma taron sauyi ko dumamar yanayi na  Majalisar Dinkin Duniya, muna bukatar ganin canji na gaske. Muna fatan hakan ya gudana musamman ta la'akari da jawabin da Shugaba Sultan Ahmed al-Jaber ya yi. Tilas mu tabbatar da ganin an amince da kawo karshen amfani da man fetur da iskar gas a takardar bayan taron da za a sanya hannu a kanta, mu kuma sanya hannu kan yarjejeniyar daina amfani da wadannan makamashi. Akwai kuma bukatar tabbatar da cewa an faara daukar matakin biyan taimaki kasashen da dumamar yanayin ke yiwa illa a matsayin kudin tallafi ba bashi ba. Mu tabbatar da daukar tsayayyen mataki na taimakawa, tare da rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa. Mu kan faid hakan a kowanne taron sauyi ko dumamar yanayi, lokaci ne da ya kamata a dauki mataki."

Shugaba Sultan Ahmed al-Jaber na Hdaddiyar Daular Larabawan na fatan za a samu mafita

Sultan Ahmed Al Jaber
Sultan Ahmed Al JaberHoto: Wang Dongzhen/Xinhua/IMAGO

Kimanin kasashe 200 da ke halartar taron dai, sun amince da a kaddamar da asusu domin tallaafawa kasashen da ke girbe abin da kasashe masu karfin tattalin arzikin masana'antu suka shuka a game da sauyi ko dumamar yanayin. A hannu guda kuma, rikici tsakanin IsraIla da kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza ya sana shugabn kasar Iran Ebrahim Raisi ba zai halarci taron na sauyi ko kuma dumamar yanayi na COP 28 da aka bude a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawan. Kafar yada labaran gwamnatin Tehran ce ta sanar da hakan, inda ta ce Raisi ya yanke shawarar kin halartar taron ne kasancewar shugaban Isra'ila Isaac  Herzog zai halarta.