1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Barazanar kwararowar hamada da guguwa

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 15, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, ana samun karuwar kwararowar hamada da guguwa mai karfi musamman a yankin Tsakiyar Asiya.

https://p.dw.com/p/4YqlW
Majalisar Dinkin Duniya | Sauyin Yanayi | Guguwa | Hamada
Guguwa mai karfi da kwararowar hamada, na illa ga lafiya da rayuwaHoto: Asaad Niazi/AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce guguwa mai karfin na da gagarumar illa ga lafiya da kuma kwararowar hamadar na kokarin mamaye yankin Tsakiyar Asiyan da Arewacin Afirka, tana mai bayyana hakan a matsayin barazana babba ga rayuwa. Hukumar Yaki da Kwararowar Hamada ta Majalisar Dinkin Duniyar UNCCD na shirin gudanar da wani taro na kwanaki biyar, gabanin babban taron sauyi ko dumamar yanayi na duniya wato COP28 da za a gudanar a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.