1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya

April 12, 2024

Amurka ta sanar da aike karin sojojinta zuwa yankin Gabas ta Tsakiya a daidai lokacin da ake fargabar rikidewar rikici a yankin bayan barazanar Iran ta kai wa Isra'ila hari ramuwar gayya.

https://p.dw.com/p/4eiAZ
Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta Tsakiya
Amurka ta aike da karin sojoji yankin Gabas ta TsakiyaHoto: U.S. military's Central Command/AP/picture alliance

Wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagone da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce Amurka ta dauki wannan mataki da nufin dakile duk wata barazana ta Iran da kuma kare muradunta a yankin.

Karin bayani: Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani

Sai dai a daidai lokacin da Washington ta sanar da wannan mataki, ministan harkokin wajen Italiya ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Iran da nufin yayyafa ruwan sanhi ga wannan sabon rikici da ke shirin daukar dumi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani: Amurka da Burtaniya sun kai sabbin hare-hare Yemen

A cikin wata sanarwa da ya fidda jami'in diflomasiyyan na Italiya Antonio Tajani ya ce ya rarrashi hukumomin fadar Taheran da ta kai zuciya nesa.

Kazalika ya kuma bukaci Iran da ta kwantar da hankulan kungiyoyi masu alaka da ita a yankin da su guji tayar da fitina don kauce wa barkewar gagarumin rikici da ba a san karshensa ba.