1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Martanin kasashen duniya kan harin Isra'ila a Siriya

Mahmud Yaya Azare AH
April 2, 2024

Babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan karamin ofishin jakadancin Iran a Damascus na kasar Syria, inda ya yi kira da a mutunta dokokin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/4eMfB
Hoto: Tasnim

 Antonio Guterres yi kira da a kaucewa duk wani tashin hankali yana mai gargadin cewa lamarin na  iya haifar da rikici a yankin da ba a taba samun kwanciyar hankali ba, tare da mummunan sakamako ga  fararen hula.

Iran ta kudirin aniyar mayar da martani kan Isra'ila

Syrien Angriff auf ein Gebäude in der Nähe der iranischen Botschaft in Damaskus
Hoto: Firas Makdesi/REUTERS

Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kazamin harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus da Isra'ila ta kai, harin da ba a taba ganin irinsa ba wanda kasashe da dama suka yi Allah wadai da shi, wanda kuma ke kara tada jijiyoyin wuya a yankin Gabas ta Tsakiya a tsakiyar yakin Gaza. A ranar Litinin makamai masu linzami guda shida da Isra'ila ta harba Siriya sun lalata ginin ofishin jakadancin Iran a Siriya  da kuma gidan jakadan Iran, inda suka kashe mutane 13,   'yan Siriya shida da 'yan Iran bakwai, a cewar gidan talabijin na kasar.

Damuwar kasashen duniya a kan harin da yakan iya haddasa tashin hankali a Gabas ta Tsakiya

Syrien Angriff auf ein Gebäude in der Nähe der iranischen Botschaft in Damaskus
Hoto: MAHER AL MOUNES/AFP

Kasar China yi Allah wadai da harin wanda ta ce ta karya dokokin tsaro ne da huldar diplomasiya yayin da kungiyar tarayyar Turai ta yi kira ga kamun kai. Shugaban diflomasiyar Iran   Hossein Amir-Abdollahianya sanar da cewa, ya aike da sako mai mahimmanci ga Amurka, wanda a matsayinta na masu goyon bayan gwamnatin IOsra'ila dole ne su dauki nauyin abin da zai biyo ba.