1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: An ji duriyar Alexeï Navalny

Abdourahamane Hassane
December 25, 2023

Jagoran 'yan adawa a Rasha Alexeï Navalny wanda ake daure da shi, wanda danginsa ba su ji duriyarsa ba kusan makonni uku,ya sake bayyana a wani gidan fursunan da ke cikin Artic yankin da ke da tsananin sanhin kankara.

https://p.dw.com/p/4aZcv
Hoto: Alexander Nemenov/AFP/Getty Images

 Navalny,mai shekaru 47,yana zaman gidan yari na shekaru 19 saboda zarginsa da ake yi masa da yi wa Rasha zagon kasa. A da ana tsare da shi a wani gidan yari da ke kusa da birnin Moscow. Kafin wannan canjin da aka yi masa watannin uku kafin zaben shugaban kasa a Rashar.   An kama Navalny  a watan Janairun shekara 2021 bayan dawowarsa daga jinya a Jamus, bayan da ya ci guba a wani yunkurin na neman hallakashi.