1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: Putin na shirin sake yin takara

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 8, 2023

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa taakara, a zaben shugaban kasar da za a gudanar a shekara ta 2024 da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4ZwHl
Rasha | Vladimir Putin | Zabe | Tazarce | Shugaban Kasa
Shugaba Vladimir Putin na Rasha, na son sake tsayawa takaraHoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Kamfanin dillancin labaran Rashan na TASS ya ruwaito cewa Shugaba Vladimir Putin ya sanar da aniyarsa ta yin tazarcen, yayin da yake karrama sojojin da suka yi yaki a Ukraine da lambar girmamawa ta ake bai wa gwarazan sojojin Rashan wato "the hero of Russia gold star" a fadarsa ta Kremlin. Putin dai ya kwashe tsawon shekaru yana shugabanci a kasar Rasha kama daga matsayin firaminista da shugaban kasa na riko, sai dai ga dukkan alamu bai shirya jan birki ba.