1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha: Putin ya bayyana nasara a yakin Ukraine

December 15, 2023

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana nasara a yakin da kasar sa ke gwabzawa da Ukraine, inda ya jaddada nasarar Mascow kan Kiev a fadan da acewarsa Ukraine ce ta takalo shi.

https://p.dw.com/p/4aB6g
Hoto: Konstantin Zavrazhin/AFP/Getty Images

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana nasara a yakin da kasar sa ke gwabzawa da Ukraine, inda ya jaddada nasarar Mascow kan Kiev a fadan da acewarsa Ukraine ce ta takalo shi.

Putin ya sanar da hakan ne a yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na akalla mutum 600 daga ciki da wajen kasar, domin tattauna nasarori da kalubalen da kasar ke fuskanta harma da batun takunkumi da kasasshen duniya suka kakaba mata.

Ya ce tabbatar da 'yancin yankunansu na tsohuwar  tarayyar Soviet ne kawai zai kawo karshen wannan yaki, kuma za a samu zaman lafiya idan har suka cimma dukkan muradunsu,  guda daga ciki kuwa shi ne Ukraine ta sanar da janyewa daga shiga kungiyar NATO.

Shugaban ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin kasar na bunkasa duk da tarin takunkuman da aka jibga mata na matsin tattalin arziki, duk kuwa da yanke hulda da kasar da kasashe yammacin duniya suka yi da Rashar, kasashen ne ke dandana kudarsu ta yanke alakar kasuwanci da Mascow.

Jawabin na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Ukraine Zelensky ka kawo wata ziyarar bazata kasar Jamus.