1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abzinawan Mali sun yi fatali da tayin tattaunawa

Abdourahamane Hassane MAB
January 3, 2024

Abzinawa da ke neman ballewa daga Mali sun nuna fargabar game da matakin gwamnatin mulkin soja na kawo karshen yarjejeniyar Algiers ta zaman lafiya. Amma Bamako na neman shirin sulhun ya zama na cikin gida.

https://p.dw.com/p/4apLE
Dubban Abzinawa ne suka amince da yarjejeniyar Algiers a 2015
Dubban Abzinawa ne suka amince da yarjejeniyar Algiers a 2015Hoto: Getty Images/F. Batiche

Shugaban mulkin sojan Mali Kanar Assimi Goita,ya kawo karshen yarjejeniyar Algiers ta zaman lafiya tsakanin kungiyar 'yan tawaye Abzinawa da gwamnatin, inda ya bayyana goyon bayan tattaunawar kai tsaye tsakanin 'yan kasar domin kawo karshen tashe-tashen hankula a arewacin kasar.

Karin bayani: Sojojin Mali na matsa lamba wa 'Yan Tawayen Azawad

A jawabinsa na shiga sabuwar shekara, Kanar Goita ya ce: " Na dauki zaɓi na fifita sulhu na cikin gida na tsarin zaman lafiya ta hanyar ba da kowace dama don jagorantar tattaunawa tsakanin 'yan Mali domin samar da zaman lafiya don kawar da  rikice-rikice a tsakanin al'ummomi''.

An dade da kulla yarjejeniyar Aljeriya

Assimi Goita ne ya yi tayin tattaunawa kai tsaye da Abzinawa
Assimi Goita ne ya yi tayin tattaunawa kai tsaye da AbzinawaHoto: Malik Konate/AFP

A shekarar 2015 ne aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin 'yan tawaye na Abzinawa. Sai dai sojojin da suka karbi mulki da karfin tuwo a shekarar ta 2020 sun yi nasarar kwace garin Kidal. Sai dai ‘yan tawayen ba su ajiye makamansu ba, maimakon haka, sun barbazu a wannan yanki na hamada da tsaunuka.

Karin bayani: Yan tawayen Abzinawa na son a yi sulhu

Kaou Abdramane Diallo jigo na jamiyyar PACP ya yi tsiokaci yana mai cewar: "Ina tsammanin yarjejeniyar Algiers ta zama marar amfani. Amma ba za mu rufe ido a kan dukkan fa'idodinta da kyakkyawan sakamakonta ba. Don haka za mu iya dorawa kan nasarorin da aka cimma a yarjejeniyar Algiers don kokarin ciyar da wannan tattaunawa tsakanin 'yan Mali gaba.. Yarjejeniyar ba duka ta yi muni ba, akwai wasu bangarori da dama na yarjejeniyar da aka aiwatar."

Abzinawa sun ki mika kai domin bori ya hau

Sakataren MNLA  Bilal Ag Acherif da tsohon ministan wajen Aljeriya Ramtane Lamamra
Sakataren MNLA Bilal Ag Acherif da tsohon ministan wajen Aljeriya Ramtane LamamraHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

'Yan awaren Abzinawa sun yi watsi da ra'ayin tattaunawar zaman lafiya da sulhu na kai tsaye da gwamnati. Amma wasu 'yan kasar Mali na ganin cewar akwai bukatar 'yan tawayen su ba da hadin kai. Hamidou Ba, magatakardan jam'iyyar Yelema ya ce: "Dole mu yi aiki don tabbatar da kowa ya shiga muhawara, dole mu nuna gaskiya don a yi wannan tattaunawa kuma dukkan 'yan kasa su yarda da tsarin. Don haka, ban ga wata illa ba, kalubalen na da yawa, amma bai wuce iyawar dukkan ‘yan kasar ta Mali ba.''

Karin bayani:Yarjejeniyar tsagaita wuta a Mali

Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya ta yi tsami tun bayan da gwamnatin Malin ta soki lamirin Algiers kan ganawar da ‘yan awaren Abzinawa suka yi ba tare da hada hannu da hukumomin Mali ba, da kuma tattaunawa da wani muhimmin jigon addini da siyasa na kasar Imam Mahmoud Dicko, daya daga cikin wanda suka bayyana a fili rashin amincewa da mulkin sojin kasar Mali.