1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Sojoji na matsa lamba wa 'Yan Tawayen Azawad

October 8, 2023

Sojojin Mali sun fara samun nasara a farmakin da suka kaddamar da nufin fatattakar 'yan tawaye da kungiyoyi jihadi da ke gwagwarmaya da makamai a Arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4XFqs
Sojojin Mali na matsa lamba ga 'Yan Tawayen AzawadHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Sojojin Mali sun yi ikirarin karbe iko da wani gari da ake kira Anefis da ke daf da birnin Kidal da ke zama tungar 'yan tawayen Abzinawa na Azawad masu gwagwarmayar raba kasar gida biyu da suka sake daukar makamai bayan yin fatali da yarjejeniyar sulhu ta birnin Algies.

 A cikin wata sanarwa rundunar sojojin na Mali mai lakabi da FAMA ta ce ta fatattaki 'yan tawaye daga garin kuma za ta doshi birnin Kidal da ke a tazarar kilomita 110, sannan kuma ta kira al'umma da su kwatar da hankula domin ta dauki matakai don tabbatar da tsaron mutane da dukiyoyinsu.  

Karin bayani: 'Yan awaren Abzinawa a Mali sun yi ikrarin kashe gomman sojoji

Mai magana da yawun kungiyar 'yan awaren ta CMA Almou Ag Mohamed, ya tabbatar wa kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa garin na Anefis na halin yanzu karkashin ikon gwamnati. Sai dai kuma ya ce birnin ba ya da wani mahinmanci a geresu kana kuma sojojin na Mali sun kame garin ne da tallafin sojojin hayan Rasha na Wagner da ya siffanta da 'yan ta'adda.

Karin bayani: Amirka ta sanya takunkumi ga jagoran Wagner a Mali

To amma gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta musanta kasancewar dakarun Wagner a cikin kasar tana mai cewa huldarta da Moscow ta ta'allaka ne a fannin horon sojojin kadai.