1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Yan tawaye na son a mutunta yarjejeniyar zaman lafiya

Abdoulaye Mamane Amadou RGB
March 7, 2022

Yan tawayen Abzinawa na son gwamnatin soja ta rikon kwarya a Mali ta fayyace manufofinta a game da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma da tsohuwar gwammnati.

https://p.dw.com/p/488DZ
Mali Sidi Brahim Ould Sidati
Hoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta CMA ta bukaci gwamnatin mulkin soja ta rikon kwarya a Mali da ta fito fili ta fayyace manufofinta game da yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan tawayen suka cimma da tsohuwar gwammnati a shekarar 2015.

A cikin wata sanarwar da ta fitar a baya, Kungiyar 'yan tawayen Abzinawa (Azawad) ta yi kakkausar suka kan yadda ake tafiyar hawainiya wajen tabbatar da yarjejeniyar da ta cimma da tsohuwar gwamnatin Malia birnin Algers na kasar Aljeriya a shekarar 2015 

Kungiyar ta ce, dole ne sojojin da ke jan ragamar mulki, su kwan da sanin cewa yarjejeniyar, alkawari ne tsakanin kasar Mali da bangaren 'yan tawaye, kana kuma hakan na da tushe a cikin tsarin shari'a.

Sanarwar kungiyar 'yan tawayen Abzinawar, ta riga ta bar baya da kura, domin kuwa tun bayan da ta fitar da ita, ta ke shan suka daga bangarorin da ke kare gwamnatin mulkin sojan ta Mali. 

Tun daga farko, ko baya ga batun ganin an tabbatar da aiki da yarjejeniyar ta zaman lafiya tsakanin 'yan tawayen na Abzinawa da gwamnati, sanarwar ta kuma bukaci da a samu hadin kai a tsakankanin bangarorin da suka rattaba mata hannu.