1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Rashin ruwan sama ya haddasa fari

Abdourahamane Hassane
April 3, 2024

Shugaban kasar Zimbabzuwe ya bayyana cewar kasarsa na cikin wani yanayi na bala'i saboda matsanancin farin da take fama da shi, da ake kira El Nino wanda zai iya saka miliyoyin jama'ar kasar cikin halin yunwa.

https://p.dw.com/p/4eP1n
Hoto: Ashley Cooper/Global Warming Images/picture alliance

Shugaba   Emmerson Mnangagwa ya ce ya ayyana yanayin bala'i na kasa saboda fari mai alaka da El Niño a lokacin wani taron manema labaran da ya yi a birnin Harare. Kasar Zimbabuwe ita ce kasa ta uku a kudancin Afirka da ta ayyana wani yanayi na bala'i, bayan Malawi da Zambiya, dangane da farin. Fiye da mutane miliyan biyu da rabi za su rasa abinci saboda rashin ruwan sama , sannan  cimmakar da aka girbe ba za ta iya ciyar da fiye da rabin al'ummar kasar ba inji shugaban kasar na   Zimababwe