1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe : Akalla giwaye 100 sun mutu saboda rashin ruwa

Abdourahamane Hassane
December 12, 2023

Akalla giwaye 100 ne suka mutu sakamakon rashin ruwa a gadun dajin kasar Zimbabwe, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin dabbobi ta bayyana.

https://p.dw.com/p/4a35j
Hoto: DW

 Tsawon lokacin rani rijiyoyin ruwa sun kafe a cikin gandun dajin Hwange, in ji asusun kula da dabbobina duniya (IFAW) a cikin wata sanarwa da ya bayyana. Gandu dajin wanda ke da wurin shakatawa wanda kuma ke da tsayin kilomita dubu14,600 na kunshe da giwaye dubu 45,000. Sannan yana da  rijiyoyin burtsatse guda 104 da ake amfani da su ta hanyar amfani da hasken rana, amma a cewar hukumar ba su isa ba wajen tinkarar matsananci zafi da ke kafe wuraren ruwa da kuma tilasta wa namun daji yin tafiya mai nisa don neman ruwa da abinci.