1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Yakin Ukraine: Zelensky ya sha alwashin galaba kan Rasha

February 24, 2024

Shugabannin kasashen yammacin duniya da kawayen Ukraine irin su Kanada da Italiya da kuma shugabar Hukumar EU Ursula von der Leyen na daga cikin wadanda suka halarci taron cika shekara biyu da yakin Ukraine a Kyiv.

https://p.dw.com/p/4cqMS
Makabartar sojin Ukraine da dakarun Rasha suka hallaka
Makabartar sojin Ukraine da dakarun Rasha suka hallakaHoto: Gleb Garanich/REUTERS

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi hasashen samun nasara a yakin da kasarsa ke gwambzawa da Rasha duk da cewa dakarun kasarsa na yaki cikin karancin kayan yaki daga yammacin duniya da kuma farmakin da Rashan ke kaiwa.

''Za mu yi nasara'', a cewar shugaba Zelensky, a yayin da yake jawabi a wannan rana ta asabar a filin jiragen sama na Kyiv da ya kasance tungar yakin tun kaddamar da farmakin Rasha a 24 ga watan Fabrairun 2022.

Karin bayani: Ukraine na neman karin tallafin daga kawayenta

Jawabin na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kai farmaki na musamman ta kasa domin murkushe duk wata barazana da ka iya tasowa daga Ukraine.

Karin bayani: Dakarun tsaron Rasha sun yi ruwan bama-bamai a Ukraine a matsayin martani

Shugaban rundunar tsaron Ukraine Oleksandr Syrsky, ya ce yana da yakinin cewa za su yi nasara, kasancewar bayan wuya sai dadi.