1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta bai wa Ukraine Euro miliyan 50

February 1, 2024

Firaministan kasar Hangri Viktor Orban wanda da farko ya yi adawa da tallafin ya bukaci kungiyar, a duk shekara ta rika nazari kan tallafin domin ganin ko tana da karfin arzikin da za ta iya cika alkawarinta.

https://p.dw.com/p/4bvte
Hoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Taron musamman na kungiyar Tarayyar Turai ta EU a wannan Alhamis ya cimma matsayar bai wa kasar Ukraine tallafin kudaden da suka kai Euro miliyan 50. Tallafin na da muradin taimaka wa Ukraine din murmure daga yakin da take yi da kasar Rasha.

A cikin shekaru hudu masu zuwa ne ake sa ran kungiyar ta EU za ta kammala tura kudaden ga kasar.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya jinjina wa gamayyar ta kasashen Turai, inda ya ce tallafin na EU cike yake da nuna 'yan uwantaka da dattaku, yana mai fatan tallafin na Euro miliyan 50 zai ba hukumomin kasar damar karfafa tattalin arzikinsu wanda mamayar Rasha ta jefa cikin mawuyacin hali.