1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sabon fatan kawo karshen rikicin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 23, 2023

Bangarorin da ke rikici a Yemen sun rungumi sabon matakin shirin tsagaita wuta gami da amincewa da matakan shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/4aX3N
Yemen | Rikici | Sulhu
Rikicin na Yemen, ya lalata wurare da dama a kasar tare da halaka mutane masu yawaHoto: picture-alliance/Photoshot/M. Mohammed

Bangarorin da ke rikici a Yemen din sun rungumi wannan sabon shirin ne, domin kawo karshen yakin da aka jima ana gwabzawa a kasar. Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Yemen din Hans Grundberg ne ya tabbatar da hakan, bayan ganawar da bangarorin suka yi a kasashen Saudiyya da Oman. Tuni jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da matakin da ya kunshi daukacin bangarorin siyasar kasar ta Yemen, kan samar da mafita a siyasance game da rikicin na tsawon lokaci tsakanin gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma 'yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran da ke rike da birnin Sanaa na kasar tun a shekara ta 2014.