1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya bukaci a kare kananan yara

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 15, 2023

Fafaroma Francis ya yi tir da yadda dubban kanan yara ke mutuwa a yankunan da ke fama da rikici na Zirin Gaza da Ukraine da kuma Yemen, yana mai kara yin kira da a samar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/4aDjU
Fafaroma Francis | Damuwa | Kisa | Kananan Yara | Zirin Gaza | Ukraine | Yemen
Fafaroma FrancisHoto: Riccardo De Luca/UPDATE IMAGES PRESS/MAXPPP/dpa/picture alliance

Fafaroma Francis ya nuna takaicinsa yana mai cewa yara sama da 3,000 ne suka halaka a yankin Zirin Gaza kawai, abin da ya bayyana da mummunan yanayi na takaici da jimami. Ya kara da cewa a Ukraine ma sama da yara 500 ne suka halaka, kana yakin Yemen da aka kwashe shekaru ana gwabzawa tsakanin sojojin kasar da 'yan tawayen Houthi ya halaka dubban kananan yara. Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta bayyana cewa sama da yara 5,000 ne rahotanni ke nunar da cewa  sun halaka a Zirin Gaza yayin da wasu dubbai suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke kai wa babu kakkautawa a yankin.