1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Nijar sun murkushe harin ta'addanci

January 7, 2024

Sojojin gwamnati a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da murkushe wani yunkurin da mayaka 'yan ta'adda suka yi na tafka ta'asa a iyakar kasar da makwabciya Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/4aw9S
Sojojin Nijar lokacin sintiri
Sojojin Nijar lokacin sintiriHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

An gano wasu fararen hula a jikkace wadanda ake ganin tsautsayi ne ya rutsa da su bayan wani artabu da ya wakana tsakanin sojojin Nijar da wasu 'yan ta'adda a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.

Sojojin na Nijar sun ce sun kai harin mai da martani ne a kan 'yan ta'addar da ke bisa babura akalla 20 da yammacin ranar Juma'a.

Mayakan na tarzoma dai sun yi kokarin afka wa sansanin soji ne da ke a Tyawa, a yankin yammacin Tillaberi iyaka da Burkina Faso.

Sojojin na Nijar ba su ba da cikakkun bayanai kan adadin fararen hular da suka jikkata ba, yayin ma da wasu ke cewa akwai mutuwa a lamarin.