1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na shirin gina wasu sabobbin tituna

July 15, 2021

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bijiro da sabuwar dabara inda yanzu manyan kamfanonin kasar za su rika gina tituna a maimakon biyan haraji.

https://p.dw.com/p/3wWnm
Nigeria Lagos | Arbeiter auf einer Baustellen | Wirtschaft
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture-alliance

A ci gaba da kokari na neman hanyar sake mai da tsohuwa yarinya ga titunan Najeriya da kusan dukkanninsu ke lalace, gwamnatin tarrayar ta kaddamar da shirin bai wa manyan kamfanoni na kasar damar gina hanyoyi a maimakon harajin da za su biya mahukunta a kasar. Akalla dalar Amurka Miliyan dubu 100, ake da bukata a shekara ga tarrayar Najeriyar da ke neman hanyar sake farfado da ababe na more rayuwa da ke lalace.  Karin Bayani:  Badakala a batun gina layin dogo 

Ga kasar da da kyar da gumin goshi ne take biyan albashin ma'aikata sakamakon rashin kudi da ke dada kamari a kasar. To sai dai kuma Abujar ta kaddamar da wani sabon shirin da a karkashinsa, manyan kamfanoni da ke biyan na haraji a kasar za su gina hanyoyi ga kasar a maimakon haraji.
Ya zuwa wannan Alhamis, kamfanin Dangote da ke zaman mafi girma cikin kasar ya rattaba hannu na gina wasu sabbabin tituna guda biyar kan tsabar kudin da ya kai Naira miliyan dubu 309. Karkashin sabuwa ta kwangilar, Dangoten zai gina titunan da tsawonsu ya kai kilomta 274 a jihohin Borno da Kaduna da Ogun da jihar Legas, kamar yadda Malam Garba Shehu da ke zama kakaki na gwamnatin ta Abuja ya fadi. Tun kafin sababbi na kwangilolin, Dangoten ya gina wasu titunan guda uku, da suka hada da Obajana zuwa Kabba a jahar Kogi da kuma Apapa zuwa Oworonshaki a birnin Lagos. 

Nigeria Autobombe Polizeistation
Wani titin shiga hedkwatar 'yan sanda a birnin MaiduguriHoto: Reuters

Karin Bayani:  Zirga-zirga ta ruwa na bunkasa a Lagos

Ko bayan Dangote, Kamfanin iskar gas na kasar LNG, ya gina manyan gadoji a babban titin da ya hade Bonny da Bodo da ke jihar Rivers a cikin yankin Niger Delta. Ana kallon sabon tsarin na iya taimaka wa tarrayar Najeriyar samun karin hanyoyin a cikin sauki ga kasar da ke daukar dogon lokaci kafin iya kammala aikin hanyar.

Tun a shekarar 1978 ne dai aka fara bada aikin hanyar Bonny zuwa Bodo, to sai dai kuma sai da ta kai ga tsoma bakin LNG ne kasar take ganin hasken kammala titin da ya tsaga ruwayen yankin Niger Delta. Duk da cewar dai kaso 90 cikin dari na kaya da mutane na zurga zurga ta titunan tarrayar Najeriya, kusan kaso 75 cikin dari na manya na tituna na gwamnatin tarrayar da aka kiyasta tsawonsu ya kai kilomita 32,000 dai na lalace.