1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗangote ya shirya magance ƙarancin man fetur a Najeriya

Usman ShehuApril 17, 2013

Alhaji Aliko Ɗangote ya ware makoɗan kuɗi don gina katafaren matatar man fetur na zamani a Najeriya, da nufin magance ƙarancin man fetur a ƙasar

https://p.dw.com/p/18H93
Lagos, NIGERIA: TO GO WITH AFP STORY IN FRENCH BY JACQUES LHUILLERY ******Nigeria-economie-energie-societe-politique*** (FILES) File picture of Nigerian businessman Aliko Dangote (L) and Femi Otedola are pictured during the opening of the second Lagos domestic airport MM2, 7 April, 2007. Aliko Dangote said that he is far more wealthier than US TV anchorwoman Oprah Winfrey which US magazine Forbes said her wealth fetches USD 1,5 billion. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI/FILES (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Aliko Dangote Aliko Dangote Hamshakin dan Kasuwa a Tarayyar NajeriyaHoto: AFP/Getty Images

Hamshaƙin ɗan kasuwan Najeriya Alhaji Aliko Ɗangote, ya sanar da cewa zai gina wani katafaren matatar man fetur na zamani a ƙasar da tafi ko wace fitar da ɗayyen mai a Afirka. Alhaji Aliko Ɗangote ya shaida wa kamfanin dillalcin labarai na Reuters cewa, an daɗe ba a gina wata matatar mai ta zamani a Najeriya ba, don haka ya kammala shirin gina katafaren matatarr mai da zai tace gangar ɗanyen mai na kimanin ganga 400.000 a ko wace rana, kafin nan da ƙarshen shekara ta 2016. Ɗangote yace idan har aka kammala wannan matar da ya ware wa kuɗi har dalar Amirka biliyan takwas don gine ta, to tabbas za ta tallafawa ɗaukacin ƙasashen Afirka kudu da Sahara, bawai ga Najeriya kawai ba. Najeriya dai tana da manyan matatun mai biyu a Fatakol da Warri, kana da ɗaya a birnin Kaduna wanda ke baiwa mutane sama da miliyan 170 mai. Babban ƙalubale a Najeriya shine samun wadataccen mai, duk da cewa itace ƙasa mafi arzikin mai a nahiyar Afirka, kuma ɗaya daga ƙasashen da suka fi sayar da man feutr a duniya. Amma ana matuƙar ƙarancin mai a ƙasar wasu lokuta sai mutane sun kwana a gidajen mai don bin layi

Lagos, NIGERIA: TO GO WITH AFP STORY IN FRENCH BY JACQUES LHUILLERY ******Nigeria-economie-energie-societe-politique*** (FILES) File picture of Nigerian businessman Aliko Dangote (L) and Femi Otedola are pictured during the opening of the second Lagos domestic airport MM2, 7 April, 2007. Aliko Dangote said that he is far more wealthier than US TV anchorwoman Oprah Winfrey which US magazine Forbes said her wealth fetches USD 1,5 billion. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI/FILES (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Aliko DangoteHoto: AFP/Getty Images

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu

RTR