1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Dangantaka tsakanin Siriya da Isra'ila da Iran

Cathrin Schaer Suleiman Babayo/USU
April 24, 2024

Mako guda kacal bayan zargin harin Isra'ila kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Siriya. Ita Siriya ta nuna babu abin da ya sauya duk da yadda lamarin yake neman zama rikicin da ya turnuke yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4f8Bq
Hari kan karamin jakadancin Iran da ke Siriya
Hari kan karamin jakadancin Iran da ke SiriyaHoto: MAHER AL MOUNES/AFP

Shi dai dan kama-karya Shugaba Bashar Assad na Siriya an nuna shi a bayyana jama'a yana harkokin da suka shafi kasar jim kadan bayan wannan hari da ake zargin Isra'ila da kai wa karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus  fadar gwamnatin kasar. Irin wannan bayyana ba abin da aka saba ba ne musamman bayan harin da ya halaka wasu sojoji a kasar da mtum yake da madafun iko.

Karin Bayani: Kasar Iran ta sha alwashin mayar da martani

Haid Haid masnain yankin Gabas ta Tsakiya a cibiyar manufofin kasashen ketere da ke birnin London na kasar Birtaniya yana ganin shugaban na Siriya yana son nuna wa duniya cewa harkokin da suka shafi kasarsa ya saka a gaba.

Siriya | Maher al-Assad da Baschar al-Assad
Shugaba Baschar al-Assad na SiriyaHoto: Ramzi Haidar/AFP/dpa/picture alliance

Bayan shafe tsawon shekaru ana yaki, zai yi wuya dakarun Siriya ace suna sauran karfin mayar da martani. Kana tattalin arzikin kasra ta Siriya ya tabarbare, domin haka zama dan-ba ruwa na a rikicin Zirin Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas, hakan ya taimaki manufofin kasashen ketere na gwamnatin Assad.

Dareen Khalifa babbar mai ba da shawara ga kungiyar sanya idanu kan rikice-rikice ta duniya tana gani duk manyan kasashen duniya sun fahimci irin sarkakiyar da ke cikin rikicin. Kungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta kasance mafi karfi daga cikin kungiyoyin da Iran take mara musu baya. Ita Iran da kungiyar ta Hezbollah duk suna gaba da Amirka da Isra'ila. Yanzu babban abin da ake tsoro shi ne barkwan yaki kai tsaye tsakanin Iran da Isra'ila.