1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaRuwanda

Paris: Shari'ar kisan kiyashin Ruwanda

Lisa Louis MAB/LMJ
November 14, 2023

Wani likita dan kasar Ruwanda na shirin fuskantar shari'a a birnin Paris na Faransa, sakamakon tuhumarsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a kasarsa.

https://p.dw.com/p/4Yo0I
Ruwanda | Kigali | Gidan Adana Kayan Tarihi | Kisan Kiyashi
Gidan adana kayan tarihi na tuna wa da kisan kiyashin da ak yi a RuwandaHoto: Hatim Kaghat/Belga Mag/AFP/Getty Images

Duk da cewa wannan likita ya musanta zargin da ake masa dai, amma wadanda suka gabatar da karar sun ce suna da kwararan hujjoji a kansa. Ranar shida ga Afrilun 1994 ta kasance wani lokaci mai ban tausayi ga tarihin kasar Ruwanda, saboda an harbo jirgin shugaban kasa na wancan lokaci Juvénal Habyarima a kan hanyarsa ta dawowa daga makwabciyar kasar Tanzaniya. Dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin ciki har da shugaban Burundi Cyprien Ntaryamira sun mutu.

Karin Bayani:Shekaru 25 da aukuwar kisan kare dangi a Ruwanda

Har yanzu ba a san ko su wane ne ke da alhakin wannan aika-aika ba, sai dai ana kallon lamarin a matsayin tushen kisan kiyashin da ya halaka mutane tsakanin dubu 500 zuwa miliyan daya. Shi dai Shugaba Habyarima dan kabilar Hutu ne da ke da rinjaye, wadanda suka zargi tsirarun 'yan kabilar Tutsi da kai harin. Kuma jim kadan bayan harin ne, aka fara kashe dimbin 'yan kabilar ta Tutsi da ma 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi. A garin Butare dai, an fara kashe-kashen ne kimanin makonni biyu bayan kashe shugaban kasar, inda aka kiyasta cewa an kashe fiye da mutane dubu 200.

Sosthène Munyemana mai shekara 68  kuma dan kabilar Hutu na aikin likitan mata a asibitin kwararru na garin Butare, amma a cewarsa, ya yi gudun hijira a tsakiyar watan Yuni zuwa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sannan ya tafi Faransa yana rayuwa da 'ya'yansa uku. A yanzu dai, ana tuhumar likita Munyemana da hannu a kisan kare dangi da kuma cin zarafin dan Adam. An ce ma ya rattaba hannu a kan budaddiyar wasikar goyon bayan gwamnatin rikon kwarya tare da wasu jiga-jigan yankin da ke hannu dumu-dumu a kisan kare dangin, sai dai lauyansa Jean-Yves Dupeux ya yi watsi da wadannan zarge-zargen yana mai cewa bita da kullin siyasa ne.

Karin Bayani: Shekaru 20 da kisan kiyashi a Ruwanda

Amma alkaliya Aurélia Devos da ta saba jin wannan muhawara saboda ta yi aiki na tsawon shekaru 10 a matsayin shugaban sashen aikata laifukan kare dangi da laifukan yaki a ofishin mai gabatar da kara na Paris da aka kafa a shekarar 2012, ta ce dukkan wadanda ake tuhuma a gaban kotun kasa da kasa kan laifuka kisan kare dangi na da irin wannan hujja. Shi ma Alain Gauthier da ya kafa kungiyar masu shigar da kara ta kasar Ruwanda (CPCR) wacce ke wakiltar masu kara 25 a shari'ar, ya nuna shakku kan hujjar matsin lambar siyasa. Ana sa ran bayyana hukuncin shari'ar da ake wa Dr Sosthène Munyemana kan hannu a kisan gillar Ruwandan, a ranar 19 ga watan Disamban da ke tafe.