1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rwanda ta fara rage cunkoson gidajen yari

June 16, 2023

Gwamnati a Ruwanda ta amince da rage yawan fursunonin da aka tsare kan laifukan kisan kiyashin da aka yi a kasar a shekarar 1994 don rage cunkoso n gidan yari da kuma sasanta juna don hadin kan kasa

https://p.dw.com/p/4ShLP
Feierlichkeiten zum Tag der Streitkräfte in Mosambik
Hoto: Estácio Valoi/DW

Fursunonin yakin na Ruwanda kimanin 2,500 ake sa ran gwamnatin Shugaba Paul Kagame za ta sako a kowace shekara kamar yadda yake cikin tsarin yafe wa juna da aka bullo da shi a kasar ya nunar. Daga cikin wadanda za a sako, su ne wadanda suka yi zaman gidan yari na akalla shekarun 20 zuwa 30.

Joseph Ndagijimana, wanda dan asalin lardin arewa ne a Rwanda, na daga cikin wadanda ke sahun gaba na samun ‘yanci, bayan kusan kammala shekarun da aka yanke masa.

Ndagijimana wanda ke zumudin ganin ya fita, ya ce yana sane da aikin da ke gabansa na sake shiga cikin al'umma, ganin irin abin da ya aikata wa makwabtansa ‘yan kabilar Tusti wadanda aka kashe dubban daruruwa.

"Ina gab da kammala zaman sarka. Don haka a shirye nake da in koma gida, in kuma nemi afuwa daga mutane, yanzu na sauya daga mutumin da aka sani a baya. Zan nuna wa ‘yan uwa ‘yan kasa sabon babi da na bude a rayuwata, inda zan hada kai da su domin yin ayyuka kyawawa tare da guje wa duk wani abu da ya yi kama da kuskuren da ya janyo min zaman da na yi a nan".

Gedenken an den Genozid in Ruanda
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Shi dai Joseph Ndagijimana na cikin mutane sama da 20,000 da aka yi ta bai wa shawarwarin sauya tunani da gwamnatin ta Rwanda ta tsara. Jean Bosco Kabanda, jami'in gidan yari ne da ke aiki a gidan gyaran hali na Kinyarwanda. Ya ce kyautata dabi'ar da aka yi musu a jarum, tsari ne da aka yi domin taimaka musu wajen na ganin sun iya sajewa cikin al'uma.

"Laccocin sake tunani da muke bai wa daurarru, an yi su ne domin taimaka musu a lokacin da za su shiga cikin al'uma. Ba mu da shakkar cewa za su kasance ‘yan kasa na gari yayin da aka sallame su. Kafin yanzun, mun sallami da dama kuma an yarda cewa abin da muka yi musu ya yi amfani. Ba mu da wata shakka a kan hakan".

Batun sakin wadanda aka kama da laifukan kisan kiyashin na Rwanda dai, ya haifar da bacin rai daga wasu da suka tsira da ransu bayan ganin irin kisan wulakanci da aka yi wa ‘yan uwansu, don haka ne suke ginin wadannan fursunonin na iya aikata wani sabon kisan na kabilanci.

Ruanda 25. Jahrestag Völkermord | Zeremonie in Kigali | Gefangene
Hoto: Getty Images/A. Renneisen

Amma kuma wasu daga cikin fursunonin ba su ji dadin jin wannan tsammani da ake yi musu ba, kamar Thomas Hategikimana wanda ya yi zaman shekaru 30 cur a daure.

"Fatana shi ne in fita in kuma hadu da wadanda na yi wa laifi, domin taimaka musu wajen warkewa daga ta'asar da na aikata. Wani abun ma shi ne ba ni da tabbacin ma ko zan samu wasu a raye. Yayin da nake fatan fita nan da shekaru biyu, a gaskiya ina matukar jin nauyin hada ido  da wadanda na yi wa laifi, shi ne ya sa nake son ganin na taimaka musu da zuciya daya. Ina fata dai za su yafe min sannan su yarda da ni".

Kisan kiyashin da ya faru a rikicin kabilancin Rwanda a shekarar 1994 dai, shi ne bala'i mafi muni da aka gani a karni na 20 a duniya, inda aka kashe akalla mutane miliyan daya cikin kwanaki 100.