1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sharhi game da zanga-zanga

Usman Shehu Usman LMJ
October 29, 2020

Zanga-zangar da aka faro da sunan kawo karshen cin zarafin da rundunar 'yan sanda mai yaki da fashi da maki wace aka sani da SARS, a Najeriya ta rikide zuwa wani abu dabam.

https://p.dw.com/p/3kbI0
Nigeria Abuja | End Sars Proteste | Demonstranten
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Duk da cewa yunkurin ya kai ga nasarar rusa rundunar, amma rashin cikakken jagorancin boren, ya sa wadanda suka shirya zanga-zangar bata rawarsu da tsalle a cewar Editan sashen Hausa na DW, Usaman Shehu Usman cikin sharhin da ya rubuta. Ya ce taken EndSARS ya shiga kafafen yada labarai a duniya, musamman shafukan sada zumunta. Rundunar SARS ta yi kaurin suna wajen azabtar da mutanen da ake zargi da aikata laifi a wasu lokutan ma har ta aika mutum lahira nan take ba tare dawani shayi ba, tamkar yadda ake jin labarin kungiyoyin mayaka na yi a wasu kasashe.

Ta kai ga rundunar SARS kan iya yanke wa mutum hukunci ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba, ta kai cewa idan kana da idon sani a runudunar SARS sai ka sa a kamo mutum a sa shi a kurku tare da 'yan fashi, misali ko da rikicin sayen fili ne ko na aure hasali ma ofishin SARS a Abuja kan cika makil da masu neman belin 'yan uwansu ko wadanda suka kawo kara. Koke kan SARS baya lissaftuwa, sau uku Sifeto janar din 'yan sandan kasar na haramtawa rundunar wasu ayyuka, an sauya masu suna sau da dama don kawo gyara, amma ba abin da ya sauya. Irin makuden kudi da jama'a ke biya don karbar dan uwansu da ya shiga hannun SARS, ko kuma wanda ke son a yi masa maganin wani abokin gaba, ya baiwa SARS karfin da basa tuna kotu ko dokar aikin dan sanda.  In za a bi kadun mutanen da SARS suka ci zarafinsu, har karshen gwamnatin Buhari ba za iya kammala adadinsu ba, ballan tana a yi batun shari'a. 

Dole kanwar naki

Cartoon SARS - spezielle Polizeigewalt
Sfeto janar na 'yan sandan Najeriya ya rusa rundunar SARS

Tura ta kai bango da gwamnati ta kasa magance lamarin, matasa musamman daga kudancin kasar sun shiga shafukan sada zumunta da lakabin EndSARS. Nan- da-nan labarin ya bazu aka fara yin zanga-zangar neman rusa rundunar. Wasu fitattun mutane suka fara cewa hakan ya yi daidai, ciki kuwa har da 'yar shugaba Buhari da 'yar mataimakinsa Osinbajo da wakilan majalisar dokoki har ma da shugaba Buhari kansa ya fito a fili ya goyi bayan koken jama'a kan rundunar kuma ya umarci a rusa ta baki daya.

Canja kala da Rashin jagora

Wandanda ke boren sun tsaga sun ga jini, suka ki komawa gidajensu, da cewar ba rusa rundunar kadai suke so ba, amma akwai jerin wasu bukatu. Dama 'yan kasar suna da dimbin matsaloli musamman na tsaro a arewaci. Kungiyoyin matasa daga fadin arewacin Najeriya suka shiga boren amma da sunan kawo karshen matsalolin tsaro, shi ma ya samu karbuwar har da Aisha Buhari uwar gidan shugaban kasa. Kasar ta fara rudewa baki daya, bata gari suka fara tarzoma da fasa gidajen yari da farma ofisoshin 'yan sanda. To a nan ne al'amura suka fara sauyawa a cewar wasu, mahukunta da suka hango hatsari idan aka bar zanga-zangar ta ci gaba, sai suka yi hayar 'yan daba wadanda akasari 'yan arewacin kasar ne, suka rusa dandazon masu boren wadanda akasari 'yan kudancin kasar ne. Su kuwa masu boren suka huce haushinsu kan wata tashar mota da akasarin 'yan arewa ke amfani da ita, suka kona motocin da ba a taba ganin barna irinta ba a tarihin birnin tarayya Abuja, wanda haka ya tabbatar da cewa masu boren ba su da jagora.

Banbancin addini da kabila ya taka rawa a rage karfin boren.

'Yan arewacin kasar sun dakatar da ta su zanga-zangar nan take domin akwai shugabanni da suke fada a ji. Sannu a hankali boren ya zama na kabilanci 'yan arewacin kasar da ke biranen kudanci aka yi ta kai masu hari da kona kadarorinsu. Babu jami'an tsaro a kan titi, zauna gari banza suka ga cewa suna iya yin komai ba hukuma, suka rika aukawa kadarorin 'yan siyasa da suke ganin su ke hana musu makoma ta gari. Gwamnati ta kira sojoji su shiga lamarin, inda dare daya aka baza su a Abuja, kuma nan take boren Abuja ya fara dushewa, to amma a can Lagos an yi zargin cewa an harbe masu bore da yawa, abin da ya jawo Allah wadai kama daga cikin gida da wajen kasar izuwa kungiyar Tarayyar Turai EU da Majalisar Dinkin Duniya. Yanzu kuma boren ya koma na wasoson rumbunan ajiye cimaka, abin da ke tabbatar da cewa tsaananin talauci shi ne tushen boren. 

Shin dama don SARS ne kawai?

DW Kommentarbild Usman Shehu
USman Shehu Usman Editan Sashen Hausa

Dama can wasu na kule da mulkin Buhari, suna cewa shugaban ya kasa cika akasarin alkawuran zabe, hakan ya sa kusan ko wane banagaren kasar a fusace. Domin an zabi Buhari ne da kyakkyawan zaton yaki da cin hanci da matsalar tsaro, matsalar da ta yi sanadin kawar da gwamnatin PDP bayan shekaru 16 kan mulki. To amma ba a je da nisa ba farin jinin Buhari ya fara dusashewa. Domin cin hanci bai sauya zani ba, matsalar tsaro kuwa a Arewa maso Yammacin kasar sai muni ta kara yi. Wannan ya sa matasan arewacin kasar tun watanni uku da suka gabata suka fara yin bore, tun a jiharsa ta asali wato Katsina. Rashin sauya hafsoshin sojan kasar bayan cikar shekarunsu na ritaya ya kara jawo shakku kan irin akidar shugaba Buhari, duk da cewa tsaro na tabarbarewa amma yaki sauya su, har majalisar dokoki ta bukaci a sauya su, amma Buhari ko a jikinsa. Wannan kuwa ba karamin bakin jini ya jawo wa mulkinsa ba, ba wai a bangaren talakawa ba har da masana da kuma jami'an sojojin da yanzu ba a yi da su.

Shin akwai tasirin da zanga-zangar EndSARS ta yi?

Ko ba komai dai akwai tasirin da zanga-zangar ta yi, na daya shi ne, gwamnatocin jihohi masu yawa sun sanar da kafa kwamitocin binciko barnar SARS. Na biyu gwamnati ta girgiza, domin shugaba Buhari ya yi sauye-sauye da yawa wanda kusan ba shugaban kasa da zai yi irinsu kasa ta yi shiru. Misali cire kudin tallafin man fetur, kara kudin wuta da mai a lokaci guda musamman bayan kuncin annobar corona. To amma sai aka wayi gari matasa na kan titi suna fasa ginin da suke so, walau na hukuma ko na jama'a. Wannan hakika ya nuna wa gwamnati matasa kan iya yin komai in tura ta kai bango. An yi zargin wasu 'yan siyasa sun so shiga cikin zanga-zangar, to amma kasancewar matasa ba su da wani shugaba, masu neman labewa da boren sun kasa samun kofar shiga.

Shawara ga gwamnati

A yanzu sauye-sauyen da ya kamata hukumomi su yi sune, duba yawan albashin 'yan siyasa, gwamnoni, 'yan majalisun dokoki da sauransu, a kara wa jami'an tsaro da bangaren ilimi kulawa ta yadda za su ba da tarbiya ta gari. Haka kuma bangaren daukar aiki, Najeriya Allah ya hore mata hazikan matasa da ke iya aiki a ko'ina a duniya, amma matsalar ita ce, sai ka ga mai digiri na biyu na sayar da doya, wani da diploma yana karbar albashin da ya fi na farfesa a jami'a. Daukar aikin gwamnati ya zama wa ka sani ba wai me ka karanta ba, wasu ma'aikatu sun rubanya wasu albashi har sau fiye da kima, duk da cewa karatu daya makaranta daya suka yi.