1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Najeriya za su samu kulawa

October 20, 2020

Bayan daukar dogon lokaci suna ji a jiki, daga dukkan alamu gwamnatin Najeriya ta karkata zuwa ga kwantar da hankali na rundunar 'yan sandan kasar, inda ta ce tana shirin kyautata mata.

https://p.dw.com/p/3kCcL
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Gwamnati za ta kyautata rayuwar 'Yan sanda a NajeriyaHoto: AFP/Y. Chiba

Kama daga sarakuna zuwa talakawan Najeriyar dai, ra'ayi yazo kusan daya game da cin zarafin da 'yan sandan ke yi ga fararen hula, da ya kamata ace ta kare. Kuma zanga-zangar neman kawo karshen rundunar SARS dai, na zaman irinta mafi girma a cikin tarihin aikin dan sandan da yake dada nuna irin jan aikin da ke gaban mahukuntan kasar.

Karin Bayani: Najeriya: Sukar rundunar 'yan sandan SWAT

Ya zuwa yanzu dai akalla jami'an 'yan sandan na SARS 37 ne ke shirin gurfana a gaban kuliya, a kokari na kare ayyukansu da ake zargin sun wuce makadi cikin rawa wajen gudanarwa. To sai dai kuma bayan wahalar, daga dukkan alamu 'yan mulki na Abuja suna shirin kwantar d hankulan 'yan sandan tare da alkawarin kula da rayuwa a ciki da ma bayan kare aiki.
A wajen kaddamar da wani ginin hukumar fanshon 'yan sanda ta kasar ne dai, Shugaba Buharin ya ce walwalar 'yan sandan za ta ci gaba da kasancewa a kan gaba a idanu na gwamnatin: "Ina rokon ku da ku ci gaba da hada kai da hukumomin 'yan sanda wajen inganta jin dadin 'yan sandan da suke aiki da ma wadanda suka yi ritaya daga aikin nasu. Bari in yabawa 'yan sandan Najeriyar kan kokarinsu wajen tunkarar matsaloli na tsaron cikin gida da kuma inganta walwala ta jami'anku. Ina ba ku tabbacin goyon bayanmu a wannan fanni."

Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Karin Bayani: Gwamanti ta baza sojoji domin dakile zanga-zanga

Ana dai ta'allaka lalacewar aikin dan sandan a Najeriyar da rashin kulawa tun daga horarwar farko ya zuwa rayuwa cikin aikin 'yan sandan da ma makoma bayan nan. Mahukuntan Tarayyar Najeriyar dai, na tsakanin tilasta jami'an 'yan sandan da nufin sauyin taku da kuma kyautata rayuwa ta jami'an tsaron da ke aiki a cikin matsatsi.