1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin cin-zarafin dan Adam a Senegal

February 15, 2024

Yayin da hankulan kasashe suka karkata kan dage zaben Senegal, wata kungiyar fararen hula ta dukufa wajen tattara hujjoji a kan wuce gona da iri da ta ce an yi wajen murkushe masu bore.

https://p.dw.com/p/4cRoS
Senegal | Jami'an Tsaro | Zanga-Zanga | Karfi | Dage Zabe | Macky Sall
ZArgin jami'an tsaro Senegal da amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangaHoto: John Wessels/AFP

Kungiyar mai suna ''CartograFreeSenegal initiative'' ta yi watsi da alkaluman da gwamnatin Macky Sall ta bayar kan rayukan da suka salwanta daga watan Yuni na 2023 zuwa wannan lokaci, tana mai ikirarin garzayawa kotu kan abin da ta bayyana da wuce gona da irin jami'an tsaro wajen murkushe masu zanga-zanga tun bayan barkewar rikicin siyasar kasar. Manyan batutuwa guda uku ne suka tayar da guguwar siyasa mafi muni a tarihin kasar Senegal ta ba a ga irinsa ba, tun daga shekarar 2021 zuwa wannan wata na Fabarairu da muke ciki.

Karin Bayani: ECOWAS: Neman mafita ga rikicin siyasar Senegal

Kama daga kiki-kaka a game da yunkurin shugaba Macky Sall na neman wa'adin mulki na uku da hana dan adawa Ousman Sonko damar tsayawa takara ta hanyar tuhumarsa a kutu, zuwa ga matakin dage zabe na ba-zata da Shugaba Sall ya dauka gabanin fara yakin neman zabe. Wadannan batutuwa sun haifar da bore a sassa da dama na kasar da ke yammacin Afrika, lamarin da janyo asarar rayuka. Kungiyoyi kare hakkin dan Adam na zargin gwamnati da yin amfani da karfin da wuce kima wajen murkushe masu bore, har ma da dasa ayar tambaya kan sahihancin alkaluman da ta fitar a game da ruyukan da suka salwanta.

Senegal | Dakar | Zanga-Zanga | Adawa | Dage Zabe
Rikicin siyasa bayan dage zabe a SenegalHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Kungiyar "CartograFreeSenegal initiative" da ta kunshi 'yan jarida na daga cikin wadanda ke tattara bayanai a kan abin da ya faru a zahiri, domin ganin gaskiya ta halinta. Kuma shugaban kungiyar Moussa Ngom ya ce, tuni ma sun nisa da fara wannan aiki. Kungiyar mai mazaunin a birnin Dakar ta ce tana bincike daya bayan na daya kisan da ake zargin jami'an tsaro da yi wa fararen hula a kasar, domin samun cikakkun bayanai daga iyaye da dangin wadanda aka kashe da kuma shaidun gani da ido na arangamar da masu zanga-zanga suka ringa yi da jami'an tsaro a fadin kasar.

Karin Bayani: Rudanin siyasa a Sengal bayan soke zabe

Babban abin takaici ma inji Ngom shi ne, yadda galibin mutanen da suka mutu sun samu raunika ne sakamakon harbin bindiga. A kullu yaumin iyalai da dama da wannan rikicin siyasa ya ritsa da danginsu, na kai kawo a cibiyar kungiya cikin tsammanin samun diyya daga gwamnati. Wannan babi dai, ya bude sabuwar mahawara kan makomar hakkin dan Adam a Senegal. Ko da a yayin tarzomar da ta barke bayan sanar da dage zabe a baya-bayan nan an zargi jami'an tsaron kasar da yin amfani da karfin da ya wuce kima wajen murkushe masu boren kalubalantar matakin, batun da ya sha suka daga Hukumar kare Hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya.