1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta shiga rudanin siyasa

Suleiman Babayo LMJ
February 5, 2024

Ana zaman tankiya sakamakon matakin Shugaba Macky Sall na soke zaben shugaban kasa da aka tsara gudanarwa a Senegal ranar 25 ga wannan wata na Febrairu, abin da ya haifar da sabon rikicin siyasa a kasar.

https://p.dw.com/p/4c4mK
Senegal Dakar Ausschreitungen der Opposition
Hoto: JOHN WESSELS/AFP

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da ke adawa da matakin Shugaba Macky Sall na jinkirta zaben shugaban kasa har sai abin da hali ya yi, a kasar da ke yankin yammacin Afirka wadda take zama inda sojoji ba su taba juyin mulki ba a yankin.

Karin Bayani: 'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal

Mutane da dama sun harzika sakamakon matakin Shugaba Macky Sall na Senegal, bayan jawabin da ya gabatar na jinkirta zaben, da aka tsara ranar 25 ga wannan wata na Febrairu musamman a birnin Dakar fadar gwamnatin kasar. Tuni 'yan adawa da 'yan gwagwarmaya suka kaddamar da yakin neamn zabe duk da matakin jinkirtawa da shugaban kasar ya dauka.

Senegal | Proteste in Dakar
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Alioune Barro yana cikin mambobin yakin neman zaben dan takara Bassirou Diomaye Faye wanda yake takara a zaben na shekara ta 2024, wanda ya nuna takaici game da tauye kundin tsrain mulkin kasar. Matakin dage zaben wani abu ne da aka tsara a cewar mai goyon bayan Ousmane Sanko daya daga cikin gaororin 'yan adawa kuma masanin na'ura mai-kwakwalwa, Walo Diaw:

Karin Bayani: AU ta nemi Senegal da ta gaggauta gudanar da babban zaben shugaban kasa

'Yan dawa sun ci gaba da yakin neman zabe kamar yadda aka tsara karkashin kotun tsarin mulki gabanin jinkirta zaben, da Shugaba Macky Sall ya yi. 'Yan adawa da dama sun nuna takaicin jinkirta zaben har sai abin da hali ya yi. A wannan Litinin majalisar dokokin kasar ta Snegal ta tattauna batun lokacin da ake artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a wajen zauyen majalisar. Kuma tuni kungiyar Tarayyar Afirka da kungiyar bunkasa ttalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, suka nuna damuwa game da yanayin siyasar kasra ta Senegal.