1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sama da bakin haure 60 sun sake mutuwa a hadarin jirgin ruwa

December 17, 2023

Akalla bakin haure 61 aka amannar sun nutse a tekun Bahar Rum, sakamakon hadarin da jirgin ruwan da ke dauke da su ya yi a ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/4aGFK
Hoto: Griechische Küstenwache/Eurokinissi/ANE/picture alliance

Bayanai na cewa jirgin na ruwa na dauke ne mutane 81 kuma galibinsu sun fito ne daga kasashen Najeriya da Gambiya gami da 'ya wasu kasashen Afirka.

Daga cikin fasinjojin jirgin da hadarin ya rutsa da su akwai mata da kanan yara, kamar yadda bayanan ke tabbatarwa.

Rahotanni na cewa jirgin ya nutse ne jim kadan bayan tashi daga Libiya saboda karfin igiyar ruwa.

Tekun Bahar Rum dai ya kasance babbar hanyar da bakin haure ke bi daga Afirka a kokarinsu na shiga Turai ta kasar Italiya.

Sama da mutum dubu biyu da 250 suka mutu a wannan shekarar a tafiyar kasadar ta teku da bakin hauren ke yi.