1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turai: Karuwar mutuwar bakin haure a teku

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 29, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa adadin bakin hauren da ke kokarin shiga Turai ba bisa ka'ida ba da suka mutu ko suka bace ya haura na bara har sau uku, tana mai cewa wajen ya zama makabartar kananan yara.

https://p.dw.com/p/4WyvR
Turai | Bakin Haure | Mutuwa
Sau da dama bakin hauren kan yi amfani da rubabbun kwale-kwale wajen shiga TuraiHoto: Borja Suarez/REUTERS

Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta nunar da cewa tsakanin watan Yuni da Agustan bana kadai kimanin mutane 990  da ke kokarin shiga Turai ne ko dai suka mutu ko suka bace, idan aka kwatanta da 334 da aka samu a shekarar da ta gabata ta 2022.