1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen larabawa na yajin aiki kan Gaza

Abdullahi Tanko Bala
December 11, 2023

Kasashen Larabawa da dama sun tsunduma yajin aiki domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza tare da kiran tsagaita wuta nan take

https://p.dw.com/p/4a1UK
Weltklimakonferenz der Vereinten Nationen (COP28) in Dubai
Hoto: Henrik Montgomery/TT/IMAGO

Ma'aikata da wuraren kasuwanci da hukumomi a kasashe da dama na Larabawa sun tsunduma yajin aiki domin nuna goyon baya ga al'ummar tare da kira a tsagaita wuta nan take. A Jordan tituna sun kasance fayau yayin da kantuna suka kasance a rufe a Amman babban birnin kasar da kuma wasu  birane da dama. Kantuna da dama sun sanya kyallaye dauke da rubutu da ke nuna suna yajin aiki.

Karin bayani: Amurka na adawa da tsagaita wuta a Gaza

A Lebanon ma makarantu da hukumomin gwamnati sun kasance a rufe. Ma'aikatar Ilmi mai zurfi a Mauritania itama ta  sanar da dage dukkan jarrabawar dalibai da kuma darusan da aka shirya gudanarwa a wannan litinin domin bai wa daliban damar shiga cikin shagulgulan da aka shirya na nuna goyon baya ga Gaza.

A yankin Gabar yamma da kogin Jordan an rufe harkokin kasuwanci da makarantu da ofisoshin gwamnati. Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa masu motocin sufuri da Bankuna da Jami'oi dun sun shiga zanga zangar

Bangarori da dama na Falasdinawa da kungiyoyin farar hula sun yi kiran gudanar da zanga zanga a ko ina a fadin duniya domin matsin lamba a tsagaita wuta a zirin Gaza.