1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Harin ta'addanci ya halaka mutane 20 a jihar Yoben Najeriya

November 1, 2023

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addar sun kai harin ne bayan da mazauna garin sun ki biyan haraji ga 'yan ta'adda

https://p.dw.com/p/4YGpl
Nigeria | Polizeifahrzeuge in Kankara
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa wani harin 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar ISWAP ya hallaka mutane 20 a Kauyen Kayayya da ke da nisan kilomita 150 daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, tare da kona wani yanki na Kauyen.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addar sun kai harin ne bayan da mazauna garin da ke sana'ar noma da kiwo suka ki biyan harajin da 'yan ta'addan suka kakaba musu.

Karin bayani:  'Yan bindga sun yi kashe-kashe a jihar Kaduna

A Larabar nan kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa ita ta kai hari wata mashaya a jiya Talata a jihar Taraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6 tare da jikkata wasu 16.

Karin bayani:  An halaka mutane kusan 50 a Benue

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa hare-haren ta'addanci sun hallaka mutane dubu arba'in a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu, tare da raba mutane kimanin miliyan biyu da gidajensu.