1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindga sun yi kashe-kashe a jihar Kaduna

March 12, 2023

Gwamnatin jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 16 a harin da 'yan bidiga suka kai garin Zangon Kataf. Hukumomi sun sanya dokar hana fita a yankin da rikicin ya shafa

https://p.dw.com/p/4OZaa
Taswirar Kaduna ta Najeriya

Yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na The Associated Press, kakakin gwamnatin karamar hukumar Yabo Ephraim ya ce, maharan sun bude wuta ne ga al'ummar kauyen Unguwar Wakili bayan arangama tsakaninsu da jami'an 'yan sanda a shingen bincike.

Tuni dai hukumomi suka sanya dokar hana fita a yankunan Ungwar Juju da Mabuhu da Ungwar Wakili da kuma Zangon Uba. . Kakakin dai ya kara da cewa, lamarin ba ya rasa nasaba da rikici tsakanin makiyaya da manoma.

A wanna lahadin dai wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a kauyen na Unguwar Wakili bisa harin na jiya Asabar domin nuna rashin jin dadinsu kan rikicin da suka ce jami'an soji sun gaza dakile aukuwarshi duk da kasancewarsu a yankin.