1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar alaka tsakanin Rasha da Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
December 4, 2023

Tawagar manyan jami'an gwamnatin Rasha ta soma wata ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar, inda ta gana da shugaban hukumar mulkin sojan kasar Janaral Abdourahamane Tiani a fadarsa.

https://p.dw.com/p/4ZmCz
Nijar | Yamai | Juyin Mulki | Gwamnati | Sojoji | Abdourahamane Tiani
Jagoran gwamnatin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Wannan shi ne karo na farko da wata tawagar jami'an gwamnatin kasar ta Rasha ke ziyara a Jamhuriyar ta Nijar, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Sai dai a lokacin da tawagar Rashan ke shirin isa Nijar, a karon farko sabuwar jakadiyar kasar Amurka ta gana da mahukuntan na Yamai tare da gabatar da takardarta ta kama aiki. A hukumance dai ba a sanar da makasudin ziyarar tawagar manyan jami'an gwamnatin Rashan da ta isa Yamai a karkashin jagorancin karamin ministan tsaron kasar Janar Yunus-bek Yevkurov ba, sai dai an bayyana cewa za ta yi taro da hukumomin tsaron Nijar.

Nijar | Juyin Mulki | Sojoji | Hulda | Rasha
Al'ummar Nijar din da dama dai, na goyon bayan sojojin da ma zuwan Rasha kasarsuHoto: AFP

Akwai dai mabambantan ra'ayoyi kan ziyarar, inda ga misali Malam Siraji Issa shugaban kungiyar farar hula ta Mojen ya nuna adawarsa. A nasa bangaren Malam Bana Ibrahim wani dan fafutuka mai goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din, fassara rububin zawarcin kasarsa da kasashen Amurka da Rashan ke a yi a matsayin wata alama ta samun cikakken 'yanci. Shi ma dai Farfesa Dicko Abdoulaye mai sharhi kan harkokin tsaro da siyasa a Nijar ya fassara lamarin da wata babbar nasara ga kasar Rasha, nasarar da ya ce ka iya barin baya da kura musamman a fannin huldar Yamai da Washington a nan gaba. Tun dai bayan juyin mulki da kuma raba gari da Faransa, al'ummar Nijar da dama ke bayyana fatan ganin kasarsu ta karfafa huldarta da kasar Rasha musamman a fannin tsaro.