1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Juyin mulkin Nijar ko Rasha na da hannu?

Hairsine Kate LMJ
August 11, 2023

Juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, ya sanya diga ayar tambaya kan ko Rasha na da alaka da shi. Ko Moscow ce ta kitsa juyin mulkin Nijar?

https://p.dw.com/p/4V4OO
Daya daga cikin masu zanga-zanga nuna goyon baya soji a Nijar
Daya daga cikin masu zanga-zanga nuna goyon baya soji a NijarHoto: Sam Mednick/AP/picture alliance

Tuni dai kasashen Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka da Nijar din, suka juya baya ga uwar gijiyarsu Faransa tare da kulla alaka da Kremlin. A Nijar din kuwa an dai hango masu gangamin goyon bayan juyin mulkin na daga tutocin Rasha, tare kuma da bayyana kyama ga Faransa da yi wa Putin fatan alheri.Wadannan alamomi na nuna kaunar Rasha da kuma zargin da mahukuntan Ukraine suka yi karara kan cewa Rasha ce ta kitsa juyin mulkin na Nijar, sun taimaka gaya wajen yada jita-jitar cewa Moscow na da hannu a juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata. Sai dai har kawo yanzu babu wata sahihiyar kafa da ta fito karara ta bayyana cewa, Rashan ce ke da alhakin hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum da ke zaman shugaban kasa na dimukuradiyya. Ko da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ma, ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa yana ganin abin da ya faru kuma yake ci gaba da faruwa a Nijar ba shi da alaka da Rasha ko sojojin hayarta na Wagner.

Karin Bayani: Kasashen Afirka na kokarin sulhunta fadan Rasha da Ukraine

Janar Abdourahamane Tiani
Janar Abdourahamane TianiHoto: REUTERS

Sojojin hayar rashan na Wagner dai, na yin hulda sosai da wasu kasashen Afirka kamar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Sudan da Mali da kuma Libiya. Ko da yake shugaban rundunar ta Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi maraba da juyin mulkin na Nijar, amma har kawo yanzu Wagner ba ta bayyana cewa tana da hannu cikinsa ba. Masana dai kamar mai sharhi a kan manufofin tsare-tsare a kamfanin tuntuba na Development Reimagined Ovigwe Eguegu na da ra'ayin cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Nijar ba ta da karfi sosai. Sai dai ya shaidawa DW cewa  "Akwai rade-radi kan cewa tun da Rasha ta fara kulla alaka da kasashen Afirka, ake ta yin juyin mulki. Sai dai wasu masu fashin baki sun yi watsi da wannan batu, suna masu cewa duk da yake Rasha na yada labaran kanzon kurege ko kuma yadda kafafen yada labaranta ke yin shirye-shiryen sukar mulkin mallaka da ma batun kyamar mulkin mallaka ya jima a yankin." 

Sanannen abu ne dai Rasha na gudanar da gangamin yada farfaganda a Afirka ciki kuwa har da Nijar. Jamhuriyar ta Nijar dai na zaman babbar kawa ga kasashen Yamma kana gida ga sansanin sojojin Faransa da Amurka masu yawa, kana sojojin na Nijar sun sanar da katse duk wata hulda da Faransan. Ana kuma ganin juyin mulkin ka iya taimakon Rasha wajen fadada muradunta a yankin Sahel, abin da ka iya ba ta karin kuri'u a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Nijar dai ta goyi bayan duka kudurorin yin tir da Rasha kan mamaye Ukraine a Majalisar Dinkin Duniyar, yayin da kasashen Mali da Guinea da Burkina Faso suka yi rowar kuri'unsu. Samun Nijar cikin kasashen da za su kare muradun Rasha, ka iya sauya wannan matsaya. Ana kuma ganin, idan Rasha ta sayar da makamai ga Nijar alakarsu ka iya inganta: Sai dai Eguegu na da ra'ayin cewa: "Ba lallai ne Rasha ta samu damar zuba babban jari a Nijar ba, sai dai za ta iya ba su makamai a matsayin hanyar karfafa dangantakarsu. Makaman ka iya bai wa sojojin da suka yi juyin mulkin damar kara karfinsu a yakin da suke da ta'addanci, kuma sakamakon da suka samu ka iya taimakonsu wajen dorewar sabuwar gwamnatinsu.

Dakarun Wagner masu kare lafiyar shugaba Faustin-Archange Touadera na Afirka ta Tsakiya
Dakarun Wagner masu kare lafiyar shugaba Faustin-Archange Touadera na Afirka ta TsakiyaHoto: Leger Kokpakpa/REUTERS

Karin Bayani: Ko Wagner na da alaka da sojojin Nijar

Duk da wadannan bayanai a kan juyin mulkin na Nijar, Lealie Varenne daraktar cibiyar nazarin huldar kasa da kasa da ke birnin Paris na Faransa, na ganin ya yi wuri a fara maganar alaka tsakanin kamfanin Wagner da kasar.Ta ce ''Jita-jita na yawo sosai kan cewar Wagner ta shiga Nijar, amma sai dai babu wasu hujjoji masu kwari kan wannan batu. Mene ne alkar sojojin da suka kifar da gwamnati da Wagner? A mahangata a yanzu dai ba su da alaka ko guda.'' A cewar cibiyar nazarin tsare-tsare ta Afirka da ke zaman wani bangare na cibiyar nazarin harkokin tsaron Amurka, wani shafin Telegram da ke goyon bayan Rasha ya yi hasashen cewa Nijar ce za ta biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso a 2022. Babban abin da ya fito fili dai, sojojin sun kifar da gwamnatin ne domin kare muradunsu. Rahotanni sun nunar da cewa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na son maye gurbin jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin Janaral Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban runduna ta musamman mai gadin shugaban kasa.