1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta haramta sararin samaniyarta ga jiragen Faransa

Abdourahamane Hassane
September 24, 2023

Hukumomin mulkin Nijar soji a Nijar sun haramta sararrin samaniyar kasar ga jiragen Faransa, ko jiragen da Faransar ta yi hayarsu, ciki har da na Air France.

https://p.dw.com/p/4WkgA
Hoto: Generalstab der französischen Armee/dpa/picture alliance

A cikin sanarwar gwamnatin ta Nijar da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Afirka da ke a Madagascar (Asecna) ta bayyyana a shafinta. Ta ce sararrin samaniyar Nijar na  bude ga dukkan jiragen kasuwanci na kasa da kasa ban da jiragen Faransako jiragen da Faransa ta yi hayarsu, ciki har da na Air France. A ranar 4 ga watan Satumba  Nijar ta sake bude sararrin samaniyarta na zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci bayan rufeshi kusan wata guda saboda barazanar kai hari da Ecowas da Faransar suka domin sake mayar da Bazoum Mohamed kan mulki.

Filin saukar jiragen sama na Diori Hamani da ke a Yamai
Filin saukar jiragen sama na Diori Hamani da ke a YamaiHoto: Zheng Yangzi/Xinhua/IMAGO