1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan jam'iyyar PDP sun yi zanga-zanga

March 6, 2023

A yayin da magoya bayan jam'iyyar APC ta masu tsintsiya ke ci gaba da biki na owamben samun mulki, 'yan lemar Najeriyar sun koma titi da nufin daukar hankali kan magudin da suke fadin an tafka a zaben shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4OKPg
Najeriya | Takara | Shugaban Kasa | PDP |  Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kaa a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku AbubakarHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Sun dai zo a cikin bacin rai kuma sun saka babbaku na tufafi a bangaren dubban 'ya'yan PDP  da suka mamaye shalkwatar hukumar zaben Najeiryar ta INEC, a karkashi na jagorancin dan takara a zaben shugaban kasar Atiku Abubakar. Sun dai shafe sa'o'i suna zanga-zangar tare da toshe kofar hukumar ta INEC, a  kokarin mika korafinsu na zargin ba daidai ba kan yadda hukumar ta gudanar tare da bayyana zabn. PDP dai ta mika wata wasika ga jami'an hukumar INEC din da kuma a cikinta suka ce, sun zayyana kura-kuran da INEC din ta aikata yayin zaben. Kokari na gyara ga kasa ko kuma neman cika buri dai, Atikun ya ce shi da magoya bayansa na shirin zama a titunan Abuja har Mahdi ya bayyana da nufin neman gyaran da a cewarsa ke zaman wajibi. To sai dai kuma da akwai tsoron zanga-zangar da ta dauki hankalin matasa, na iya rikidewa ya zuwa rikici a nan gaba cikin kasar da ta sha ba dadi  a cikin sunan zanga-zanga.

Najeriya | Abuja | Atiku Abubakar
Magoya bayan dan karar shugaban kasa a jam'iyar adawa ta PDP sun yi zanga-zangaHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Gift dai wata matashiya ce da ta taka rawa a cikin zanga-zangar da ta kai ga mamaye harabar INEC din, kuma ta ce sun dawo daga rakiyar hukumar da ke shirin yin zaben gwamnoni a karshen mako. Koma ya zuwa ina Atikun da magoya bayansa ke shirin su je da nufin neman sauraronsu dai, daga dukkan alamu 'yan lemar na takama da hukuncin kasashen duniya da ke dada dawowa daga rakiyar sakamakon da hukumar ta bayyana a makon jiya. Hajiya Baraka Sani dai na zaman daraktar gangamin magoya baya a cikin yakin neman zaben na Atiku da kuma ta ce, gangamin nasu na da burin aiken sako a cikin neman sauya hukumar zaben da ke nuna alamu na karkata zuwa ga masu tsintsiya. 'Yan kwanaki da ke tafe dai na da muhimmanci ga hukumar zaben da ke fatan kai wa ya zuwa wankin suna da kila ma kimarta ciki da ma wajen kasar, bayan zargi na gazawa da kila ma tsomin bakin da ke kara fitowa fili daga sassa dabam-dabam ciki da ma wajen Tarayyar Najeriyar.