1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu ya ba da haske na kyakkyawar fata

Abdullahi Tanko Bala LMJ
March 1, 2023

Abubuwan ba-zata, sune suka yi ta faruwa a kullum a Najeriya, a lokacin da kuma bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar a karshen mako. Hakan ta faru a aikace da kuma a sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/4O8RZ
Najeriya | Zabe | 2023 | Shugaban Kasa| Bola Ahmed Tinubu
Sabon zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

A sharhin nasa da ya rubuta daidai lokacin da sabon shugaban kasa ke shirin karbar ragamar mulki a Najeriyar dai, Editan sashen Hausa na DW Abdullahi Tanko Bala ya ce: Ga tsarin dimukuradiyyar da ke samun ci-gaba, za a iya bayyana zaben Najeriya na 2023 a matsayin sahihi. Idan aka kwatanta da sauran zabuka shidan da suka gabata, yawancin abubwan ba-zata da aka samu na nuni da sahihancinsa. Ga misali, rashin nasarar manyan 'yan takara a wajen da suka fi karfi, na zaman babban abin al'ajabi. Jam'iyyun adawa sun taka gagarumar rawar gani a wurare da dama, wanda rashin daidaito tsakanin manyan 'yan siyasa ya haifar. Wasu abubuwa sun fara buduwa: Neman mafita a tsakanin masu zabe, wanda hakan ya tabbatar da dimukuradiyyar kasar.

Karin Bayani: Obi ya lashe zaben shugaba kasa a Lagos

Jan-kafa a bangaren masu zabe, babban abin damuwa ne da bai kamata a yi watsi da shi ba. Kaso 18 cikin 100 bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da kaso 37 cikin 100 a zaben da ya gabata. Ya ce: Ina son yin amanna cewa, hakan na da alaka da yadda wasu masu zaben suka sauya wuraren zama. Ko kuma tashe-tashen hankula, wanda suka hana gudanar da zabukan a wasu jihohi. Sai dai a zahirin gaskiya da yawan 'yan Najeriya, suna da gagarumar matsalar rashin yadda idan aka zo batun zabe, wanda hakan ya haifar da jan-kafa. Idan aka ajiye batun adadin masu kada kuri'a, shugaban kasar da aka zaba ya fito ne daga jam'iyyar da mambobinta ke da mabambantan ra'ayoyi a kansa. Babban zaben, ya nunar da hakan.

DW-Hausa | Abdullahi Tanko | Edita
Abdullahi Tanko BalaHoto: DW

Na yi amanna cewa, wadanda suka zabi Bola Tinubu sun yi imanin cewa shekarunsa da yanayin lafiyarsa ba za su zama tarnaki ba. Akwai 'yan Najeriyar da za su fi son wani mai karancin shekaru, sai dai kwarewar da Tinubu ke da ita ka iya taimaka masa wajen yin abin da ya dace. Aikin gwamnati wani faffadan abu da ke bukatar aiki tare. Tinubu na da tarihin samar da abokan aikin da suka dace, wadanda ba sa bayar da kunya. Koda yake, zai fi kyau a yi taka-tsan-tsan wajen saka buri. Babu shakka, ya kamata a tuna yadda al'ummar Najeriya da dama suka saka irin wannan buri ga shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari a yayin da yake yakin neman zabe. Sai dai kash! ba a faye kawo gyara a kan abin da aka tarar a baya ba a siyasayar Najeriya. Sakamakon haka abubuwa sun ci gaba da gudana kamar a bayan, koma fiye.

Karin Bayani: Zaben Najeriya: Sakamakon zabe na tayar da kura

Duk yanda za a kai ga fata, mutum zai iya tunanin cewa Tinubu zai fahimci matsalolin da Najeriyar ke ciki domin kawo gyara. Abu ne mai kyau, yin kyakkyawan fata. Wata babbar tambaya ita ce. ko Tinubu zai iya wakiltar matasan Najeriya, wadanda a yanzu suka kasance mafiya rinjaye cikin masu zabe? A jawabinsa na farko bayan da ya lashe zabe, ya ayyana bai wa bukatun matasa muhimmanci. Abdullahi Tanko Bala ya kara da cewa: Ni na yi imanin cewa, akwai bukatar kawo gyara a bangaren yadda matasan Najeriya za su samu abin yi. Hanya daya ta cimma wannan burin, ita ce ta samar da wani tsari. Ya kamata shugaban kasar ya yi aiki tare da matasa masu ilimi da wayewa, domin amfana da kwarewarsu. Hakan zai sanya siyasar kasar ta zamo mai tafiya da kwararrun matasa kana abin sha'awa gare su, kuma zai bayyana a tsarin gwamnatinsa. Abin jira a gani shi ne: Ko Tinubu zai bi wannan hanya?