1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An sun ceto yaran da aka sace a Sokoto

March 23, 2024

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto mutane 17 ciki har da kananan yara 16 da mace daya, wadanda aka yi garkuwa da su a yankin arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4e3sT
Sojoji sun ceto yaran da aka sace a jihar Sokoto da ke Najeriya
Sojoji sun ceto yaran da aka sace a jihar Sokoto da ke NajeriyaHoto: AP/dpa/picture alliance

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Edward Buba ya ce sun rigaya sun mika mutanen da aka kubutar ga gwamnatin jihar Sokoto ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Tun ranar 9 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kama daliban a makarantar Islamiyya da ke jihar Sokoto, kwanaki kalilan bayan sace yara sama da 250 a wata makaranta da ke Kuriga a jihar Kaduna.

Karin bayani:Kaduna: Ko daliban da aka sace za su tsira? 

A shekarun baya-bayan nan dai, barayin daji sun yi garkuwa da daruruwan yara da dalibai a sakamakon tabarbarewar tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da kuma yankin tsakiyar Najeriya. Sai dai Janar Buba ya ce sojojin kasar ba za su taba gajiyawa ba har sai an ceto dukkan 'yan Najeriya da aka yi garkuwa da su.

A nasa bangaren ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce kwanaki goma da suka gabata, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci jami'an tsaro da ke neman daliban da su tabbatar da cewa ba a biya ko sisin Kobo a matsayin kudin fansa ba.