1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Hana amfani da janareta a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 15, 2023

A wani kokari na kare matsalar sauyin yanayi da alkinta muhalli, gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin dakatar da amfani da injinan janareta domin samar da hasken wutar lantaraki a kasar.

https://p.dw.com/p/4WOnI
Najeriya I Lagas | Janareta | Haske | Wutar Lantarki | Muhalli | Hayaki | Illa
Mutane da dama a Najeriya na dogaro da janareta domin samun hasken wutar lantarkiHoto: Saheed Olugbon

Wannan dai wani yunkuri ne da gwamnatin Najeriyar ke son yi saboda yadda matsalolin sauyin yanayi ke kara bayyana a fili, kama daga yawaitar ambaliyar ruwa ya zuwa fari da ko a damunar bana ana fama da shi. A kwai kuma tsananin zafin rana da kwararowar hamada, duka a dalili na dumamar da duniya ke yi saboda hayakin da ake alakanta wa da injinan janaretan ke haifarwa da kuma na masana'antu.

Kare muhalli ta hanyar dashen itatuwa

Amfani da injinan janareta ya zama wata al'ada a Najeriyar a matsayin hanyar samun hasken wutar lantarki saboda gazawa daga bangaren gwamnati, domin injin janaretan ya zama kusan gidan duk wadanda suke da hali na motsin aljihunsu. Koda yake gwamnatin na hangen samun nasara in an samu aiwatar da wannan shiri a kasar musamman wajen alkinta muhalli, to sai dai akwai damuwa a kan yadda za a yi da masu masana'antu da suka dogara a kan injin janairetan domin ayyukansu. Najeriyar dai na cikin halin tsaka mai wuya tsakanin bukatar alkinta muhalli da kuma matsalar hasken wutar lantarkin, wanda hukumar kididigar jama'a ta bayyana cewa mutane milayn 11da dubu 400 ne daga cikin 'yan kasar sama da milyan 200 ke samun wuta lantarki.