1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Durkushewar wutar lantarki a Najeriya

Uwais Abubakar Idris RGB
June 13, 2022

Najeriya ta sake fuskantar durkushewar wutar lantarki a sakamakon yadda manyan biranen da dama suka kasance cikin duhu na tsawon awanni.

https://p.dw.com/p/4Cdy2
Afrika Elektrizität Nigeria Afam VI
Hoto: Getty Images/AFP/F. Plaucheur

Wannan shi ne karo na hudu da ake samun wannan yanayi, inda gaba daya ba wutar lantarki a kasar. Daya bayan daya ne dai kamfanonin rarraba wutar lantarkin da aka maida su hannun ‘yan kasuwa suka rinka fitar da sanarwa suna bai wa masu amfani da wutar hakuri kan cewa daukacin tsarin ya durkushe har kasa, kama daga Abuja, zuwa shiyyar Kano da Enugu duka labarin daya ne na durkushewar wuta lantaraki. Bayanai na nuna cewa an yi asarar Megawat dubu 3317 na wutar a lokaci guda.

Afrikaische Stromversorgung
Najeriya na fama da tsadar kudin wutar lantarkiHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Bayanai sun nuna cewa matsaloli ne suka hadu, ga na rashin wadataccen ruwa a tashoshin samar da wuta lantarki da ke Jabba da Kainji, sannan injinan da ke amfani da makamashin gas don samar da hasken wutar, ana yi masu gyara, abin da ya sanya fiye da sau shida ana fuskantara wannan matsala a cikin wannan shekarar.

Lagos Nigeria
Manyan birane sun fuskanci daukewar wutar Hoto: Sunday Alamba/picture-alliance/AP Photo

Duk da cewa an fara maido da wutar a sassan da biranen Najeriyar ciki har da Abuja hedikwtar gwamnatin Najeriyar. Durkushewar wutar lantarki, babban lamari ne ga Najeriya a matsayinta na kasar da tattalin arzikinta ke fuskantar koma baya, musamman a fanin masana’antu da gudanar da harkokin kasuwanci na yau da kullum.

Najeriya dai ta mayar da harkar samarwa da sayar da wutar lantarkin a hannun ‘yan kasuwa baya ga makudan kudin da ta zuba a harkar, amma zargin cin hanci da rashawa ya sanya yi wa matsalar katutu inda har yanzu aka kasa samun ci gaban da ya kamata a fannin samar da wutar lantarkin a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.