1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban EFCC a komar DSS din Najeriya

June 15, 2023

A wani abu da ka iya kara jefa yaki da cin-hanci a Tarayyar Najeriya cikin rudani, sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar EFCC Abdurasheeed Bawa.

https://p.dw.com/p/4SdvQ
Najeriya | Abdulrashid Bawa | EFCC
Shugaban hukumar EFCC ta Najeriya da aka dakatar Abdulrashid BawaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Abdulrasheed Bawa dai, na zaman shugaba na hudu cikin guda biyar a hukumar EFCC da ke yaki da cin-hanci da rashawa da ya bar aiki a cikin yanayi maras kyau. Duk da cewar gwamnatin kasar ba ta fito fili wajen bayyana nau'in laifukan da ake zargin shugaban EFCC din da aikatawa ba, dakatar da shi kasa da wata guda da hawa mulki na sabuwar gwamnatin na nuna irin gwarman rikicin da ke a hukumar. Duk da cewar EFCC na zaman hukuma mafi tasiri a cikin yakin hancin dai, tana kuma kan gaba a siyasar cin-hancin da ta mamaye kasar a tsawon lokaci. Kama daga binciken shugaban kasar ya zuwa rawa a cikin harkokin majalisa dai, ana zargin Bawa da dumu-dumu cikin harkokin siyasa kasar.

Zanen Barkwanci | EFCC | Ibrahim Magu
Ba dai Abdulrashid Bawa ne na farko da aaka dakatar a matsayin shugaban EFCC baHoto: DW/ A. Baba Aminu

Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun na siyasa da ku ma ya ce Bawan ya wuce makadi cikin rawa a aikin nasa. Koma ya take shirin kayawa a cikin rikicin yakin hancin dai, akwai zargin ita kanta hukumar ta kafu ne ba cikin neman mafita a kan cin-hancin ba. Maimakon hakan dai EFCC din na zaman karen farautar 'yan mulki na kasar, wajen danne abokai na adawa da kila kokarin shafa musu kashin kaji. Abun jira a gani dai na zaman mafitar yaki da cin-hanci cikin bakar siyasa ta kasar, kuma bukatar kawo karshen matsalar da ke zaman barazana mai girma ga ci-gaban Najeriyar.