1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MSC: kalubalen kwararar bakin haure a duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
February 16, 2024

Wani binciken kasa da kasa kan tsaro ya nuna kwararar baki ko hijira a matsayin babban kalubale da ya zarta barazanar da ake fuskanta na yaki daga Rasha, a lokacin da ake gudanar da taron tsaro a Munich.

https://p.dw.com/p/4cVOL
Deutschland | Münchener Sicherheitskonferenz | Kamala Harris
Hoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Duniya a shekarar 2024 na fuskantar "koma baya a siyasar kasa da kasa tare da fuskantar habakar tashe-tashen hankula da rashin tabbas a fannin tattalin arziki." Wannan shi ne abin da shugaban taron tsaro na Munich Christoph Heusgen ya rubuta a cikin sabon rahoto bayan bincike da aka gudanar da shi kamar duk watan Fabrairu. Hasali ma dai, manyan jami’an tsaro da kwararrun 'yan siyasa daga ko’ina cikin duniya na haduwa a birnin Munich da ke kudancin Jamus don tattaunawa kan duk matsaloli da suka shafi tsaro a duniya. Kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky na daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron MSC daga 16 zuwa 18 ga Fabrairun 2024.

Karin Bayani: Duniya na fuskantar barazanar rashin tsaro

A shakarar da ta gabata dai, rahoton taron tssaro na Munich ya bayyana yakin Rasha da Ukraine a matsayin barazana mafi girma ga tsaro musamman a kasashen G7. Amma a halin yanzu wannan matsayi ya sauya inda jama'a ke kallon manufofin ketare na Rasha a matsayin wata barazana. A daya hannun kuwa, mazauna wadannan kasashe na dauka kwararar bakin haure ko hijira da matsalar sauyin yanayi ya haifar a matsayin babban hadari ga duniya. Wannan ya fito fili ne a cikin binciken da aka gudanar kan halin da duniya ke ciki yanzu, inda MSC ta tuntube mutane 12,000 a  kasashen G7 da kuma Ukraine da Brazil da Indiya da Chaina da Afirka ta Kudu.

 Tobias Bunde, daraktan bincike da manufofin tsaro na taron MSC a Munich ya yi tsokaci a kan wannan batu:

Karin Bayani: Shugabanni na halartar taron tsaro a Munich

Mahalarta taron tsaro na Munich a Jamus
Mahalarta taron tsaro na Munich a JamusHoto: THOMAS KIENZLE/AFP

" Taken rahotonmu na bana tamkar wani gargadi ne da ke nuna cewar za mu iya shiga cikin hali na rashin tabbas. A ganinmu, manyan masu fada a ji a siyasar duniya a kusan ko'ina na nuna rashin gamsuwa da abin da suke dauka a matsayin rashin daidaito na rabon fa'idodi a matsayin kasaa da kasa. Za ku iya ganin cewar kasashen da ake kira na kudancin duniya sun yi imani da cewa ba su taba ci gajiya yadda ya kamata ba,  inda wasu ke wawushe na su rabon."

A Ukraine, binciken ya nemi sanin sanin "sharadi mai karbuwa don tsagaita bude wuta," inda kashi 92% na wadanda aka tuntuba ke kiran da a janye sojojin Rasha gaba daya daga kasar da kuma yankin Crimea. Kashi 12% ne kawai ne suka amince Crimea ta kasance karkashin ikon Rasha. Sannan fiye da kashi biyu bisa uku na son a shigar da Ukraine cikin gaggawa a Kungiyar tarayyar Turai da kungiyar tsaro ta NATO. A karkashin taken "Lose-Lose", rahoton tsaron da ke zama na goma ya nuna cewar hadarin da ke tattare da rikicin soji a tsakanin Chaina da Taiwan ya karu matuka. Alal hakika, tsoron kasar Chaina ta dogaro da kanta ya karu musamman a Japan da Indiya da Amurka da Jamus da kuma Faransa. Amma a cikin kasashen G7, jama'a da yawa sun yi imanin cewa kasashensu za su rasa tasiri da wadata cikin shekaru goma masu zuwa, kuma sakamakon binciken ya ce al'ummar kasashen G7 na sa ran samun karuwar tasirin kasar Chaina da kasashen masu tasowa fiye da kasashensu.

Karin Bayani: Taron birnin Munich a game da tsaro

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens StoltenbergHoto: Matthias Schrader/AP/picture alliance

Ga ma abin  da Tobias Bunde, daraktan bincike da manufofin tsaro na taron MSC a Munich ke cewa a kan wannan batu:

"Chaina da Indiya sabanin sauran, suna da kyakkyawan fata game da makomar kasarsu. Japan ita ce ta fi kowa rashin kwarin gwiwa, inda kashi 10% ne kawai ke da yakinin cewa kasarsu za ta kasance mafi aminci da wadata. Kuma nan da shekaru goma masu zuwa, Amurka za ta fi samun kwarin gwiwa. Amma mafi yawan kasashen Turai a zahiri suna sara tare da duba bakin gatari game da makomarsu, kuma bayananmu sun nuna cewa 'ya'yan manyan kasashen yammacin duniya na ganin sauran kasashe za su kara samun karin karfi kuma kasashensu za su rasa karfinsu a cikin shekaru goma masu zuwa."

 Akasarin wadanda aka tuntuba sun bayyana rashin gamsuwa da yanayin tattalin arzikin duniya, duk da rage dogaro da Asiya da sauran yankuna na duniya da kasashen Turai suka yi a baya-bayan nan. Amma kamfanonin Jamus suna ci gaba da saka hannun jari sosai a Chaina tare da bijire wa kokarin Berlin na rage ayyukansu a kasar.