1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Munich ya yi hasashen rikice-rikice

February 18, 2022

Taron tsaro na shekara-shekara a birnin Munich na kasar Jamus an fitar da rahoton yanayin tsaro da ake ciki da ya nuna irin barazana na tunani gami da zahiri na yuwuwar samun rikice-rikice a duniya.

https://p.dw.com/p/47GQF
Münchner Sicherheitskonferenz MSC
Hoto: ANDREAS GEBERT/REUTERS

 

Wannan taro na birnin Munich na zuwa lokacin da zaman tankiya ya karu da tunanin yadda Rasha ta jibge sojoji a Ukraine tana iya yin kutse. Sai dai jami'in diflomasiyya Wolfgang Ischinger yana mai cewa kwai bukatar duba duk abubuwa da suke faruwa a bangrori dabam-dabam na duniya ganin irin matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassan duniya. Rikice-rikice da hanyoyin magance su na daga cikin abin da rahoton tsaron ya kunsa da ake wallafa kwanaki gabanin fara taron na birnin Munich na Jamus duk shekara, kuma taken rahoton na bana shi ne "Sauya zaman rashin tabbas da ake fuskanta." Rahoton ya duba irin rashin tabbas da wasu al'ummomi baya ga kalubale iri-iri da suke fuskanta. Rahoton tsaron wannan shekara ya duba rayuwar fiye da mutane 12,000 da suke zama a sassa dabam-dabam na duniya da irin kasadar da suke fuskanta. A Jamus ga misali sauyin yanayi na kan gaba cikin kasadar, yayin da a Amirka ake damuwa kan yuwuwar hari ta kafar intanet, sannan a Rasha rashin daidaito tsakanin mutane ke kara tusa tsaro. Kasar Indiya ta kasance kasa ce da mutane ke damuwa kan samun rikicin mai nasaba da makaman nukiya. A Afghanistan an shiga rudani tun bayan janyewar dakarun kasashen dunyia, sannan a Mali da yankin Sahel na Afirka gami da gabashin Afirka da yankin Gulf lamura ke kara dagulewa.