1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Na'urorin zaben Najeriya sun gaza

Ubale Musa SB/USU
April 11, 2023

A yayin da kura take kara lafawa bayan manyan zabukan tarrayar Najeriya, wasu bayanan sirin da ke fitowa daga kasar Amirka sun tabbatar da hannun hukumar zabe wajen gazawar na'urar BVAS mai tantace masu zabe na kasar.

https://p.dw.com/p/4Pv0P
Zaben Najeriya na 2023
Zaben NajeriyaHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

 

Bayan nan da aka tsinta a cikin yanan gizo dai sun ce hukumar zaben Najeriya ta INEC ta san injunan na BVAS ba za su yi aiki ba tun ma kafin zabukan kasar cikin watan Fabrairu. Wasu bayanan da jami'an leken asirin Amirka suka tsinta a ranar jim kadan kafin babban zaben shugaban kasar dai sun ce jami'an tsaron farin kayan DSS sun samu bayanai na jami'ai na hukumar zaben cewar na'urar BVAS tana fuskantar matsaloli sakamakon kumbura na batirin da take dogaro da shi wajen aikin.

Karin Bayani: Atiku ya kalubalanci zaben shugaban kasa

Zaben Najeriya na 2023, birnin Lagos lokacin zaben shugaban kasa
Zaben NajeriyaHoto: BENSON IBEABUCHI/AFP

Duk da cewar dai kasar ta Amirka ba ta bayyana matsayin ta bisa sabbabi na bayan da ake tallaka da jami'ai na leken sirrinta ba, bayanan sun ambato mafi yawa na injunan BVAS din basa aiki a jihar Rivers sakamakon matsalar ta batiri. Haka kuma, jami'ai na hukumar zaben sun ambato wasu matsalolin na'urar a wasu sassan yankin arewa maso gabas cikin kasar. Tuni dai sabbabin bayanan suka fara jawo dagun hakarkari cikin fagen siyasar Najeriya.

Haka ita ma hukumar ta tsaron farin kaya ba ta ce uffan ba bisa sabbabin bayanan da suka ambato jami'anta kai tsaye. Auwal Musa Rafsanjani dai na zaman shugaban gamin gambizar yan kallon cikin gida a yayin zaben kuma ya ce abin da ke fitowa yanzun na kama da kokari na cin aman ta kasa. Miliyoyi na 'yan Najeirya dai suna kallo na'urar BVAS a matsayin gada tsakanin kasar da kai wa ya zuwa ingantaccen zabe.