1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takarar PDP ya kalubalanci zaben Najeriya

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2023

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya na babbar jamm'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa ya kalubalanci nasarar da jam'iyya mai mulki ta yi.

https://p.dw.com/p/4P4jI
Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Abubakar wanda ya mika korafinsa ga kotun daukaka kara a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar a Talatar wannan makon, ya bi sahun takwaransa na jam'iyyar Labour Peter Obi da ya zo na uku a zaben na 25 ga watan Fabarairun da ya gabata. 

Matakin 'yan takarar biyu dai, ka iya zama na shari'ar da za ta dauki dogon zango kafin kammalata da nufin kalubalantar nasarar da tsohon gwamman jihar Lagos, kana dan takara a jam'iyya mai mulki da ya samu nasara da kusan kaso 37 cikin 100 na kuri'un da aka kada Bola Tinubu.

Cikin korafin da ya shígar din, Atiku Abubakar ya bayyana cewa sakamakon zaben haramtacce ne ganin cewa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ba ta bi dokokin zaben ba wajen saka sakamakon ta hanyar amfani da na'ura.