1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: MDD na neman ba'asin mutuwar dan fafatuka

April 21, 2024

Majalisar Dinkin Duniya na son a kaddamar da bincike kan wani dan fafatuka, Siraj Dughman da ya mutu a hannun jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/4f1ox
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Libiya, Abdoulaye Bathily
Hoto: Eskinder Debebe/UN Photo/Handout/Xinhua/picture alliance

Hukumar da ke sa ido kan rikicin Libiya na Majalisar Dinkin Duniya, UNSMIL ta bukaci hukumkomi da ke gabashin kasar da su kaddamar da bincike mai zaman kanshi kan mutuwar wani dan fafatuka da aka tsare shi tun a bara.

Siraj Dughman dai ya mutu ne a hannun jami'an tsaro a sansanin soji da ke garin Rajma a cewar hukumar. Hukumar tsaro ta cikin gida ta Libiyar ta fitar da sanarwar cewa, Dughman ya mutu ne sakamakon fadowa da ya yi ta kanshi a yayin da yake hawa saman tagar wani bandaki a lokacin da yake yunkurin tsere wa daga sansanin a ranar Juma'ar da ta gabata.

Karin bayani: Libya ta saki wasu mayaka 

Hukumar ta kara da cewa, an tsare Dughman ne sakamakon wasu taruka da aka tattauna batun hambarar da kungiyoyin siyasa da kuma sojoji, kuma ana tsare da shi ne bisa doka da ya yi daidai da dokokin kare hakkin dan Adam.

Tun a shekarar 2023 ne aka kama Dughman da wasu mutum hudu, inda hukumar ta zargi cewa an gaza gurfanar da su a gaban shari'a.

A lokacin da yake jawabi a gaban kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wakilin majalisar a Libya, Abdoulaye Bathily ya nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar bacewar mutane da kame mutane ba bisa shari'a ba a Libiya.