1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Mutane 11000 suka mutu

Abdourahamane Hassane
September 15, 2023

MDD ta kaddamar da wata gidauniya ta neman kudade sama da dalar Amurka miliyan 71 don samar da agajin gaggawa ga wasu mutane dubu 250,000 da bala'in ambaliyar ya shafa a kasar Libya.

https://p.dw.com/p/4WMmn
Libyen | Überschwemmung und Hochwasser in Libyen
Hoto: AFP/Getty Images

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta yi kiyasin cewar dubban daruruwan mutane ne ke bukatar agaji bayan mummunar ambaliyar. Kasar ta Libiya  da ke arewacin Afirka ta fuskanci wata mummunar guguwa a ranar Lahadin da ta gabata inda madatsun ruwa guda biyu suka fashe a kusa da birnin Darna, suka share sassan birnin, mai yawan jama'a  dubu dari.Yanzu haka samun shiga yankin da bala'in ya afku yana da matukar wahala, bayan lalacewar hanyoyi da gadoji, da kuma layukan wutar lantarki da na wayar tarho a manyan yankuna, inda akalla mutane dubu 30 suka rasa matsuguni yayin da wasu sama da du 11 suka mutu.

Libyen Überschwemmungen
Hoto: Abdullah Mohammed Bonja/AA/picture alliance