1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kwanaki 100 na gwamnati

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 7, 2023

Yayin da sabuwar gwamnatin Najeriya ta cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, al'ummar kasar na kokawa da tsananin talauci da kuncin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.

https://p.dw.com/p/4W5Kv
Najeriya | Peter Obi | Labour | Bola Tinubu | APC | Atiku Abubakar | PDP
Peter Obi na Labour da Bola Ahmed Tinubu na APC da kuma Atiku Abubakar na PDPHoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Al'ummar Najeriyar da dama na ganin matakin furta janye tallafin man fetur da sabon zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi, shi ne sanadin duk wasu wahalhalu da kuncin rayuwa da suke fuskanta. Bayan batun janye tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin ta yi, akwai kuma batun kasuwar canjin kudin kasashen ketare da gwamnatin ta ce nan ma ta zare hannunta ta kuma bar kasuwar ta yi halinta.

Wadannan matakai dai sun janyo farashin kayan masarufi ya yi tashin gauron zabi, inda al'umma ke kokawa kan yadda a yanzu ba kowanne gida ne ake iya samun abinci ba saboda tsabar talauci. Haka nan ma man fetur ya yi tsada, inda ma'aikata ke kukan ba sa tsadar ababen hawa wajen zuwa aiki. A yanzu da gwamnatin ta cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, ra'ayoyi sun banbamta kan yadda lamura ke wakana a kasar da ke zaman mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

A lokacin da gwamnatin ta cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin ne kuma, kotun sauraron kararrakin zabe ta yi fatali da karar da manyan jam'iyyun adawar kasar biyu na PDP da Labour suka shigar suna kalubalantar nasarar da dan takarar jam'iyyar APC mai mulki Shugaba Bola Ahmed Tinubun ya yi. A yanzu haka dai 'yan takarar jam'iyyun biyu Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour, sun sha alwashin daukaka kara zuwa kotun koli.