1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tinubu ya kwana 100 a mulki

September 6, 2023

Bayan shafe kwanaki 100 a kan karagar mulki, daga dukkan alamu sabon shugaban Tarayyar Najeriya na ci gaba a karatun laluben neman al-kiblar diflomasiya ga kasar da ke cikin rudani.

https://p.dw.com/p/4W1lh
Najeriya | Abuja | Bola Ahmed Tinubu | ECOWAS | CEDEAO
Shugaban Najeriya kana shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO Bola Ahmed TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

A kokarin daukar zafi ne dai sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dauki ragamar jagorancin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, tare da neman kasashen Mali da Burkina Faso da ma Guinea su sanya ranar koma wa ga tafarkin dimukuradiyya. To sai dai kuma juyin mulkin Jamhuriyar Nijar ne ya zamo kalubale mafi girma ga Shugaba Tinubun da ke tunanin aiken sako, amma kuma ke kallon siyasar cikin gida mai zafi. Wa'adin mako guda na sake mayar da Bazoum Mohamed kan mulki dai, na neman zama watanni biyu ba tare da kwalliya ta mayar da kudi na sabulu a bangaren Najeriyar ba. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batu na siyasa, kuma ya ce sabon shugaban na neman zama dan sandan jan kunne a daukacin yankin na yammacin Afirka. Sabon fata dai a yayin da Shugaba Tinubun ke kokarin zare ido a cikin yankin na Afirka ta Yamma dai, daga dukkan alamu Najeriyar a cikin ikon Tinubun ta shiga karatun rudu a nahiyar Afirka da ma siyasar Gabas da yammacin duniya mai zafi.

Najeriya | Abuja | Bola Ahmed Tinubu | BRICS
Kungiyar BRICS, ta yi wa Najeriya nisaHoto: Sergei Bobylev/TASS/dpa/picture alliance

Duk da kasancewar mataimakin shugaban kasar a taron Rasha dai, Najeriyar ta kare da zama 'yar kallo a kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa Cikin Hanzari wato BRICS da ke tunanin ciniki ko ba Turawan Yamma. Duk da kasancewar mafi yawan kasashen na BRICS na takama da hajjar man fetur, kasashena Masar da Habasha ne suka yi nasarar samun gurbi a kungiyar mai tasiri. Ambasada Bala Mohammed dai na sharhi cikin batun diflomassiyar da kuma ya ce kasar tana bukatar kallon tsaf, kafin jefa kafa cikin siyasar ta BRICS. A baya dai Najeiryar ta dau matakin babu ruwa cikin batun diflommasiya a duniya, kafin karkata ga tattalin arziki cikin neman sauki. To sai dai kuma kasancewar Tinubu a Indiya kasa ta uku da ya ziyarta a kwanaki 100 na mulkin nasa domin kallon taron kasashe na kungiyar G20 ta masu karfin tattali na arziki dai, na nuna alamun karkatar kasar zuwa ga Turawan Yamma a shekarun da ke tafe. Najeriyar dai a fadar Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da ke zaman ministan harkokin kasashen wajen kasar, za ta karkata zuwa ga wasu bukatu guda hudu cikin rawar da take shirin da ta taka a duniya a shekaru hudun da ke tafe.