1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Najeriya

Binta Aliyu Zurmi MAB
September 6, 2023

Kotun sauraren kararakin zabe a Najeriya za ta yanke hukunci kan karar da manyan 'yan takarar neman shugabancin kasar a zaben 2023 suka shigar gabanta na neman a soke nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

https://p.dw.com/p/4Vzv6
'Yan takaran shugaban kasa a zaben 2023: Peter Obi da Bola Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

An kwashe kusan watannin bakwai, alkalai biyar na sauraran korafe-korafe daga jam'iyyar PDP mai adawa da ta zo na biyu a zaben da kuma ta Labour Party wacce ta zo na uku. Atiku Abuubakar na neman kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta soke shi gabaki daya bisa zargin tafka magudin zabe, yayin da Peter Obi shi ma ya bukaci a soke zaben don a gudanar da wani sabo.

Karin bayani: Najeriya: Korafe-korafe kan sakamakon zaben 2023

Za a watsa zaman kotun kai tsaye a gidajen talabijin din kasar da sauran kafofin watsa labarai. Jam'iyyar APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ba ta da wani fargaba a kan yadda hukuncin kotun zai kasance, kuma ta yi amannar cewar ita za ta samu nasara a shari'ar. 

Ko ma ya hukuncin kotun ya kaya, jam'iyyun PDP da LP na da dama sake daukaka kara zuuwa kotun koli.